Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu gungun ‘yan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP ta sha ɓarin wuta daga hannun rundunar sojin Nijeriya a ranar Laraba bayan wani da suka kai karo na biyu sansanin soji da ke Rann a ƙaramar Hukumar Kala Balge a jihar Borno.
Manhaja ta rawaito muku cewa ‘yan ta’addan, sun sake dawowa sansanin ne ƙasa da awanni 48 bayan harin farko da suka kai kan sansanin da ƙarin wasu guda uku a jihar Borno a tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata.
A cewar Zagazola Makama, mai bibiyar lamuran rashin tsaro a yankin tafkin Chadi, ‘yan ta’addan sun yi basaja ne a matsayin Fulani makiyaya, sai dai rundunar sojin ta ɓaro jirginsu tare da nasarar kashe wasu dama a cikinsu.
Majiyar ta kuma ce, sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan ne da taimakon wani jirgin yaƙi na sojin saman Nijeriya wanda ya tilasta musu komawa da baya.
Wannan ya sa an samu nasarar kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan da lalata motarsu ƙirar Hiluɗ a yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Duk da majiyar ba ta iya bayyana adadin waɗanda aka kashe ba, amma a yanzu komai ya lafa kuma sansanin na cikin aminci.
Wannan nasara da rundunar sojin Nijeriya ta samu na zuwa ne bayan tabbacin da kwamandan rundunar Operation Haɗin Kai, manjo-janar AE Abubakar, ya bayar a ranar Talata na cigaba da murƙushe ‘yan ta’addan da ba su shawarar su miƙa kansu ko a kawo ƙarshensu.
Sai dai har yanzu masu ruwa da tsaki a Nijeriya ba su ce komai ba kan sabbin hare-haren da ‘yan ta’addan ke kai wa sojoji.
