Yanar gizo riba ce ko akasi ga tsaro?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun ba soshiyal midiya akwai wannan kulli a zuciyar abokan gaban Hausawa don alakar Hausawa da addini. Duk tarihin miyagun kashe-kashe a baya ai an san wadanda su ka aikata kama daga zubar da jinin Zangon Kataf, Yelwan Shendam har ma rikicin da ke faruwa a cikin Jos kafin ma na Gonin Gora. Duk Hausawa da a ke kira JASAWA sun san su waye ke kai mu su farmaki da kona gidajensu. A Jos ne masu kisan za su yi taro su raba gadon dukiyar Jasawa wai in sun kashe su, za su ci bulus, wannan ya ce shi zai zauna a gidan Alhaji wane ko ya mallaki motar Malam wane. Kai duk wanda ba dan Jos ba, ba lallai ya san zurfin fitinar nan ba. Har gobe akwai inda Jasawa ba sa iya shiga hakanan su ma masu iƙirarin ‘yan ƙasa akwai sassan da ba sa marmarin zuwa don gudun abun da su ka shuka jiya. Akwai shekarar da su ka kai farmakin kisan kare dangi kan dandazon musulmi a masallacin idi a Jos. Ina Jasawa sun san wannan labarin. Waye ya taba fitowa ya ce ba a kyauta ba. Yau irin miyagun nan ne a soshiyal midiya su ka dinka rigar Hausawa.

Me laifin matafiyi da ya zo wucewa ta garinku. Wallahi sun kashe mutane a kan hanyar nan da ragargaza namansu da bunne su don kawar da shaida. Wani lokacin nisan kwana daga Allah kan tserar da wasu matafiyan in sun zo wucewa don hakika akwai matasa ‘yan gayawa-jini na wuce da ke marmarin su kashe. Kawai ka tare mutumin da ba ka sani ba ka kashe shi don addininku ba daya ba ne. Ba ma kisan kadai ba, wulakanta gawar. Akwai fa wani ma da matasan nan su ka make shi ya faɗi sai wani mugu ya suntumo wani katon dutse ya ribza ma sa a tsakar ka! Wasu ma kan dau duwatsu su yi ta dandatsa naman gawawwakin matafiyan da su ka kashe. Shin akwai wani babba a masu kisan da ya taɓa magana da nuna hakan ba daidai ba ne? to haƙiƙa waɗannan na kan gaba a ‘yan Hausa zalla da su ka hau soshiyal midiya su na ruruta fitinar kabilanci da zuga mutane su dau makami.

Gaba daya harkar Hausa zalla fa tunanin wasu mugayen mutane ne da su ka lura harshen Hausa na da tasiri kuma da shi malamai Musulmi ke wa’azi wajen hada kan musulmi, su zama masu kaunar Allah da manzonsa. Damar boye suna a soshiyal midiya don ruruta wannan fitina ta zama mai sauki ga miyagun nan. Wallahi in Hausawa ne ba wanda zai boye sunansa ko amfani da hoton yaudara don bayyana ra’ayi. ‘Yan kalilan da ke fitowa ma a karkshin kasa su ke kunna wutar kuma sun ga za su iya zagin Shehu Mujaddadi su kwana lafiya. Nan gaba tabbas mutanen nan za su daina fakewa da zagin Fulani wajen sukar musulunci zuwa kan sahabbai ko ma su isa kan Manzon Allah mai tsira da aminci. Tunaninsu tun da su na boye ai ba mai iya gano su balle ya dau mataki a kan cin mutuncin masu mutunci da su ke yi. Duk mai zabar kabila ta fi addini to kun san addinin da ya ke bi. Dama su addini ba wani abu ba ne a wajensu amma kiyayyar masu addini ita ce dabi’arsu, da ita a ka gina su kuma da alamu a kan wannan kiyayya za su mutu.

In wanda ba ya mutunta addini ya zunduma ma ka ashar ai ba mamaki don dama haka ya ke ji a ransa ya kashe ka ma ba komai. Fakewa da ‘yan ta’addan daji wai su na kashe su, ba haka ba ne don ko kazarsu ba a taba kashewa ba. Hasalima iyayen gidansu zuriyar IPOB ke samar da dabarun satar mutane ga barayin daji da kuma yi mu su safarar makamai da miyagun kwayoyi. Duk wani mai zarmiya da ya ce ba su Chinedu ba ne ke kashe mutane a Arewa to shi ne Chinedun kura da fatar akuya. Kullum sai kara bude shafukan karya da sunan Hausawa su ke yi. Su fito fili in ba wani abu su ke boyewa ba. Duk wanda ya boye kansa ya shigo nan ya na caccaka ko korafi to mun san ko waye kuma dubunsa zai cika.

Gaskiyar magana sai dai dan ta’adda ko mai zuga tada fitina ya fake da wani addini ko kabila don samun mafaka ko dalilin aikata mugun aikinsa. Ba yadda za a yi mai yin sallah da gaskiya ya zama dan ta’adda sai dai gafalalle ko munafuki. Kazalika ba mabiyin addinin kirista na gaskiya da zai yi ta’addanci ko tare matafiya ya sheke su kuma ya iya kafa hujja a BIBLE. Kazalika kawo kabila ko kabilanci a lamuran ta’addanci mugun zalunci ne da wasu ke yi don cimma muradin kiyayya da ta yi kanta a zuciyarsu. Kama daga maciyin amana Chukwuma Nzeogwu da ya bude wuta a gidan firimiya Sir Ahmadu Bello ya bindige Sajan Daramola Oyegoke don kin amincewa ya harba babbar bindigar tankar yaƙi don ruguje gidan Arewa da Sardauna ke ciki kowa ma ya mutu; ya shiga gidan ya bindige Sardauna har hakan ya shafi matarsa Hafsa.

Mu gangaro kan Nnamdi Kanu wanda ya yi ta hura wuta lallai sai mutanensa sun dau makami sun yi ta kashe-kashe don a kafa Biyafara da karfin tsiya. Ya yi sanadiyyar kashe daruruwan mutane ciki da jami’an tsaro da ‘yan Arewa musamman Hausawa. Sai kwatsam yayin yanke ma sa hukunci, ‘yan iƙirarin Hausa zalla su ka yi tsayin daka har da kiran zanga-zanga wai lallai sai an sake shi. Ba mu yi mamaki ba don dama Kanu ya kwan biyu ya na kiran a hargitse da yaƙi a Arewa.

Duk barayin dajin nan na da manyan magabatansu da su ka koyo dabarun satar mutane daga wajensu da samun miyagun kwayoyi da makamai. Kun tuna kasurgumin mai satar mutane da safarar miyagun ƙwayoyi Chukwudumeme Onwuamadike wanda a ka fi sani da EVANS ya fi kowa shahara da satar mutane kuma an cafke shi a 2017 bayan a daya daga ayyukansa ya nemi fansar dala miliyan 2. Hamshaƙin mai hannu da shuni ne na kudin jini kuma haifaffen Nnewi da ke jihar Anambra. DCP Abba Kyari ya cafke shi kuma an gurfanar da shi gaban kotu a Lagos da samunsa da laifi. Ya yi sanadiyyar kashe mutane da daman gaske.

Cikin miyagun masu kashe mutane ba gaira ba dalili akwai kwamandan IPOB Ifeanyi Eze Okorienta wanda a ka fi sani da GENTLE DE YAHOO wanda ke jagorantar kashe-kashe a gungun rundunar kisan gilla ta IPOB wato ESN. In ransa ya ɓaci ya kan bindige hatta yaransa kamar yadda mu ke gani a fim din Indiya. Mu dawo nan Binuwai mu tuno ta’addancin satar mutane da kisan gilla barkatai na Tarwase Akwaza da a ka fi sani da Gana haifaffen Gbeji da ke Katsina-Ala a jihar Binuwai. Gana don tsananin kashe-kashe har a na cewa ya kan bace bat ya bayyana kuma in an ambaci sunansa mutane kan shiga rawar dari da firgita don dan-gayawa-jini-na wuce ne. Da kyar sojoji su ka yi nasara a kan sa a 2020.

A Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya an fara samun matsala ne bayan lafawar Boko Haram a Arewa maso gabar. Mun san miyagu da su ka bunƙasa daga satar shanu zuwa satar mutane. Haƙiƙa a Arewa da can sai dai ‘yan kwanta-kwanta a kan titi ba ma wasu gaggan ‘yan fashi ba duk wannan an yi simogan ɗabi’ar daga kudu ne. Al’ummar musamman jihar Zamfara za su fi zama shaida kan yadda matsalar nan ta fara har ta zama gagarumar matsalar tsaro.

Mun san labarin Buharin daji wanda tuni ya sheka lahira. Ga Dogo Gide, ga Halliru Sabubu na lahira, ga Kachalla Ali na lahira, ga Baleri na lahira da sauran su da lokaci ne kawai a ke jira. Sunan wanda ya fi shahara a kafafen labaru Bello Turji wanda ƙaramin yaro ne da har banan nan shekarunsa 32 don an haife shi a Shinkafi jihar Zamfara a 1994. Har fa a ka gama yaƙin Saddam na farko ba a haife shi ba. Har a ka yi yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar ba a haife shi ba, har a ka yi zaben 12 ga Yuni 1993 na Abiola ba a haife shi ba. Mu na fatan ranar da ya gamu da gamonsa a samu zaman lafiya mai dorewa. Wato abun da ke damuna yaranmu da wasu ma Turji ya grime su nesa ba kusa ba don akwai wanda bana ya ke 18-20 amma su ke hawa soshiyal midiya su na zunduma ashar don ba su san tarihin Arewa ba sai karyar da su Nnamdi Kanu su ka shayar da su ta yanar gizo da ƙiyayya ta ba gaira ba dalilin adalci da su ka samu daga iyayensu da jama’ar ƙauyukansu.

KAMMALAWA

Ba yadda za a yi Bahaushe ya zama Nnamdi Kanu ne zai fadawa ma sa abun da zai yi ko wasu Gwarawa da su ka ɗinka rigar bagaye ta Hausawa ne wai za su haska mu su yadda za su yi rayuwa. Kullum su kan jefi duk wanda su ke son a hallaka da kalmar AGWAI wacce ba Hausawa ke amfani da ita wajen ambaton Fulani ba, kalma ce ta kabilun Arewa ta tsakiyar Nijeriya da wasu masu bahaguwar manufa ke kira MIDDLE BELT. Wallahi ba fada tsakanin Hausawa da Fulani amma akwai ƙiyayya ga Hausawa daga maƙiya addini da ke jin haushin ƙarfin riƙo da addini na Hausawa.

By ukarofi