Yanzu-yanzu: Ba a ga wata Saudiyya ba, za a yi sallah ranar Juma’a

Spread the love

Hukumomi a ƙasar Saudi Arabia sun sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ko’ina cikin ƙasar a wannan rana, lamarin da ya sa aka yanke shawarar cika watan Ramadan kwana 30.

Sanarwar ta nuna cewa sakamakon rashin ganin watan, za a ci gaba da azumi gobe domin cika kwanaki 30 na watan Ramadan, kafin a gudanar da bikin Ƙaramar Sallah a ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026.

Kwamitocin duban wata da cibiyoyin lura da taurari a faɗin ƙasar sun gudanar da bincike a wurare daban-daban, amma duk da haka ba a samu tabbacin ganin jinjirin watan Shawwal ba.

Hukumomin addini sun jaddada cewa wannan mataki ya yi daidai da koyarwar Musulunci, wadda ta tanadi cika watan Ramadan idan ba a ga watan Shawwal ba.

Don haka, Musulmai a ƙasar da sauran sassan duniya da ke bin sahun Saudiyya za su gudanar da bikin Eid al-Fitr a ranar Juma’a, bayan kammala azumin watan Ramadan.

A ƙarshe, malamai da hukumomi sun yi kira ga al’umma da su ci gaba da ibada da addu’o’i, tare da fatan Allah Ya karɓi azumi, salloli da sauran ayyukan alheri da aka gudanar a watan mai alfarma.

By Babaji