
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na III a yau Laraba yayin wata ziyarar ƙarfafa alaƙar Nijeriya da Birtaniya.
Duk da cewa shugaban ƙasar ya ziyarci Birtaniya a lokuta da dama tun bayan hawansa mulki, wannan ita ce ziyarar aiki ta farko tsakanin ƙasashen cikin kusan shekaru 37.
Tinubu ya samu rakiyar matarsa, Oluremi Tinubu da sauran muƙarrabansa na Gwamnatin Tarayya.
An karrama su da sarawa ta bindiga da ake kira da
’42-gun salute’ daga sojojin sarki na ‘Royal Horse Artillery’.
Gabanin haka Yarima William da Gimbiya Catherine sun gana a shugaban Nijeriyar da Uwargidan tasa a otal ɗin Fairmont, inda daga nan ne suka garzaya Fadar ‘Windsor Castle’, suka gana da Sarki Charles, sannan ya nuna musu kayayyakin tarihi musamman masi alaƙa da Nijeriya.




