Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Duk watan Ramadan mu kan tafi hutu daga fitar da labarai don yin ayyukan ibada – Zainab Abdullahi
A kowacce shekara a lokaci irin wannan na Ramadan, musulmi a ko’ina a duniya na shagaltuwa da ayyukan ibada da neman kusanci da Allah, marubuta adabin Hausa su ma sukan jingine ayyukan rubuce-rubuce na nishaɗi da faɗakarwa da suke yi, zuwa ga tilawar Alƙur’ani, da faɗakarwa kan al’amuran addini, da koyar da girke-girke ga mata. A irin wannan lokaci mambobin ƙungiyar marubuta ta Jajirtattu Writers Association suna ware tsawon watan Ramadan don gudanar da shirye-shirye da suka shafi Tambayoyin Musulunci da karatun Alƙur’ani. Wannan wani ɓangare ne na ayyukan alheri da taimakon juna da ƙungiyar ta saba, domin dasa wa mambobinta tsoron Allah da son juna. A ganawar da wakilin Manhaja Blueprint Abba Abubakar Yakubu, ya yi da shugabar ƙungiyar, Malama Zainab Abdullahi da aka fi sani da Maman Ihsan, ta bayyana masa irin nasarorin da ƙungiyar ke samu, da ƙalubalenta.
MANHAJA: Za ki gabatar mana da kanki.
MAMAN IHSAN: Sunana Zainab Abdullahi wacce aka fi sani da Maman Ihsan a duniyar marubuta. Kuma ni ce shugabar ƙungiyar Jajirtattu Writers Association.
Ki gaya mana wani abu daga tarihin rayuwarki.
Ni haifaffiyar garin Kontagora ce daga Jihar Neja. Na yi karatuna na firamare a makarantar Model School da ke Kontagora. Bayan na kammala na shiga makarantar sakandiren ‘yam mata ta jeka-ka-dawo, da aka fi sani da GGDSS, na kuma kammala a Kwalejin Horar Da Malamai ta FCE Kontagora. Bayan na kammala ne na yi aure a garin Minna cikin Jihar Neja. Alhamdulillah. A ɓangaren karatun addini kuma na yi saukar Alƙur’ani Mai Girma tun ina sakandire. Ina da aure da yara.
Yaya aka yi ki ka samu kanki a sahun marubuta?
Na samu kaina a sahun marubuta sakamakon yawan karance-karancen littattafai da nake yi tun ina ƙarama. Bana mantawa lokacin ina sakandire, na ji wasu suna hirar wani littafi da suka karanta to, ina sauraren su ne sai na ji sha’awar karanta littafin ni ma. Sai nake tambayar a ina zan samu littafin, mai ba da labarin ta ce da ni aro ta yi, kuma har ta mayar wa mai shi. Daga nan ne nake tambayar ina ake sayar da littafin, aka sanar da ni. Bayan an sanar da ni ne na je na fara saya ina karantawa. Daga nan kuma sai na fara fuskantar ƙalubale daga gida, inda iyayena suka riƙa min faɗan yawan karanta littattafan Hausa, cewa ba ya bari yarinya ta mayar da hankali ga karatu.
A dalilin haka ne sai na riƙa yin karatun littafin a ɓoye, musamman da daddare idan ina kwanta a ɗaki, idan na ji motsin Mamana za ta shigo sai na yi sauri na ɓoye littafin ƙasan filo na yi likimo kamar ina barci. A haka har watarana na fara tunanin rubuta nawa labarin. A lokacin da nake sanar da wata ƙawata, sai cewa ta yi ba zan iya rubutu ba, don ba abu ne mai sauƙi ba, ta ga waɗanda suka fara suka kasa ƙarasawa. Ni kuma na ce zan iya, in sha Allahu. Don ina da yaƙini a kan hakan. Daga nan na samu sabon littafi da fensir na fara rubuta labari. A taƙaice dai sai da na cika littafin rubutu na 60 leaɓes guda biyu da labarina. Daga nan idan ina zaune ba na komai kawai zan zauna na dinga ƙirƙirar labari ina rubutawa.
Bayan na yi aure na cigaba da karanta littattafan marubutan Hausa a waya. Ba zan manta ba, a wani zauren marubuta da na shiga a WhatsApp na ji wata na cewa a tura musu littafi su karanta, sai na ce musu ina da labarin da zan rubuta ko suna so na rubuta? Suka ce, E, suna so. Daga haka ne na fara rubuta littafina na farko mai suna ‘Inteesar’ a waya, cikin ikon Allah abu kamar wasa sai na ga ana ta bibiyar labarin bayan an raba gayyata ga masu sha’awar shiga zauren da nake sake labarin. Ban taɓa tunanin labarin zai ja hankalin masu karatu haka ba, don a gaskiya littafin ya karɓu sosai, har zauruka biyu na buɗe saboda yawan masu son bibiyar littafin.
Mene ne yake baki sha’awa da harkar rubutun adabi?
Zumunci da kaunar juna. Da samuwar fasaha da dabarun sanin rayuwa na zamantakewa. Har’ila’yau na haɗu da mabambantan mutane daga wurare daban-daban, sun zamo tamkar ‘yan’uwa a gare ni. Ina samun girmamawa sama da tsammanina, har watarana nake ta mamakin yadda lokaci guda na yi tasiri a zukatan mutane.
Ko za ki ba mu tarihin kafuwar ƙungiyar Jajirtattu Writers Association, da manufar kafata?
ƙungiyar Jajirtattu Writers Association, ƙungiya ce da aka kafa domin taimakawa ƙananan marubuta masu tasowa da sabbin marubuta da ke neman sanin dabarun rubuta labari da sanin ƙa’idojin rubutu. An kafa ƙungiyar Jajirtattu shekaru biyu kenan a cikin watan Fabrairu, 25 ga watan 2024.
Babban dalilin da ya sa na kafa ta shi ne saboda na taimakawa marubutan da suke sha’awar fara rubutu, amma ba su da ƙungiya ko kuma ba su da damar shiga sakamakon ba su da kuɗin yin rijista da wasu ƙungiyoyin. Bana mantawa a baya kafin na buɗe tawa ƙungiyar lokacin ina cikin wata ƙungiya akwai wasu mutane uku sabbin fara rubutu da suka yi mini magana kan cewa suna son su fara rubutu, amma ba su san yadda za su fara ba, sai nake ba su shawara da ƙwarin gwiwa. Bayan sun rubuta labarin suka tura mini na duba na gani to, abin ka da sabbin fara rubutu, ba su san ƙa’idojin rubutu ba gabaɗaya, a cakuɗe rubutun nasu yake. Sai na ba su shawarar su nemi ƙungiya ta ƙwararrun marubuta su shiga, hakan zai taimaka musu wajen sanin dabarun rubutu da kuma sanin ƙa’idojinsa ta yadda saƙon su zai isa ga masu karatu yadda ya kamata. Amma sai matsalar rashin kuɗin yin rijista ya hana su shiga.
Wannan dalilin ne ya sa na fara tunanin hanyar da zan taimaka musu, na ga ba wata hanyar da ta wuce na buɗe tawa ƙungiyar. Wannan shi ne silar buɗe ƙungiyar Jajirtattu Writers Association. Amma kafin na buɗe sai da na yi bincike sosai daga manyan marubuta na tabbatar ba wata kungiyar da ke da irin wannan sunan kafin na saka wa ƙungiyata sunan.
Da mutane biyar na fara kafa kungiyar, wato ni da wasu mambobi biyar. A hankali sai mutane musamman sabbin marubuta suka riƙa nuna sha’awar suna son shiga ƙungiyar. Haka na fara tafiyar da kungiyar ni kaɗai, ina yi musu gyare-gyare, na kuma nuna musu inda suka yi kuskure. A dalilin haka na jinginar da nawa rubutun, domin harkokin ƙungiyar ba ya bari na in yi rubutuna.
Gabaɗaya lokacina yana tafiya ne wajen gyaran rubutun mambobin ƙungiyata, don idan na ce zan yi rubutu ba na samun lokaci, wasu ma ba na samun yi ma su a ranar sai ya kwana kafin na samu damar yi musu. Daga baya na yanke shawarar samun wani ƙwararren marubuci da zai riƙa taimaka mana ta hanyar koyar da darasi da kuma dabarun rubutu. Sai wata ta bani lambar wayar marubuci Yusuf Yahaya Gumel, wanda na nemi taimakonsa akan ya dinga koyar da mu darasi akan sanin dabarun rubutu. Allah cikin ikonSa sai kuwa na yi sa’a ya amince. Yanzu haka yana koyar da mu darasi, kuma Alhamdulillahi kwalliya tana biyan kuɗin sabulu.
Daga nan ne kuma marubuciya Maryam Anas Burando (Momeeyn Irfaan) ta shiga ƙungiyar. Sai bayan ta shiga ne na ɗan samu sauƙi, kasancewar tana taya ni hidimar ƙungiyar, har na ba ta matsayin mataimakiyata. Sannu a hankali waɗanda suka iya muka fara yaye su su ma suka fara taimaka mana da duba wasu ayyukan na sabbin marubuta masu shigowa. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙungiyar Jajirtattu ta yi suna a duniyar marubutan onlayin wanda ko hira ake yi akan ƙungiyoyi da zarar na ce ni ce shugabar ƙungiyar sai ka ji ana cewa, au dama ke ce! Ta hakan nasan ƙungiyar ta yi suna fiye da tunanina. Kuma na ga mun yi yawa mun kai mu tamanin, a lokacin. Kuma akwai ƙwararru waɗanda hakan ya sa na naɗa wasu na ba su muƙami a cikin kungiyar daga cikin ƙwarrrrun da muke da su.
Sai dai fa ƙungiyar Jajirtattu ta masu rubutu ce ba ta haɗin kan marubuta ba. Domin duk wacce ta daina rubutu cire ta muke yi daga cikin ƙungiyar. A yanzu haka muna da mambobi sittin da takwas.
Wacce gudunmawa ƙungiyar ku ke bayarwa ga cigaban mambobinta?
Jajirtattu na bai wa mambobinta damar cigaba ta hanyar haɓaka harkar adabi. Tana kuma taimakawa mambobinta wajen koya musu dubarun shiga gasa da bayar da ƙwarin gwiwa. Kungiya ce da ke cicciɓa mutane daga ƙasa zuwa sama.
Duk wannan nasarar ta samu ne daga irin sadaukarwa da Yusuf Yahaya Gumel yake bayarwa wajen fito da tsare-tsaren cigaba, tare da ba mu ƙwarin gwiwa, wajen koya mana abubuwan da za su bunƙasa rubutunmu. Har yanzu yana fama da iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin mun zamo na musamman, kuma da gaske ana samun sauyi a cikin tafiyar.
Akwai wasu fitattun marubuta a cikin ku da suka samu wasu nasarori a harkar rubutu?
A gaskiya babu wasu fitattun marubuta a ciki, domin ƙungiyar marubuta ta masu tasowa ce. Sai dai a ciki akwai waɗanda suke shiga gasa kuma suna samun nasara. Akwai waɗanda suka karɓu sosai, kuma suke samun mabiya da labaran da suke rubutawa, har ana jin amon su a duniyar rubutu.
Zan so na san irin abubuwan da ku ke gabatarwa a matsayin ku na ƙungiya don raya ƙungiya?
Masha Allah! Muna gabatar da shirye-shirye daban-daban masu alfanu na cigaban adabi, da suka haɗa da shirin ‘Daga Makaranta’, shirin ‘Daga Wasiƙunku’, shirin ‘Kasuwanci’, shirin ‘Tambaya da Amsa,’ shirin ‘Labaran Ban Dariya’, da kuma shirin ‘Karatun Alkur’ani Mai Girma’.
A shirin ‘Daga Makaranta’ muna bayar da dama ga duk wani makaranci ya turo da sunan labarin da ya karanta da abubuwan da ya burge shi a labarin.
A cikin shirin ‘Daga Wasiƙunku’ muna bayar da dama ga duk mai wata matsala ta rayuwa ya tura za a kawo, ba tare da an bayyana sunansa ba, a ba shi shawara. Haka kuma a shirinmu na ‘Kasuwanci’ muna tattaunawa da marubuta da ke gudanar da wasu harkokin kasuwanci, don jin abubuwan da suke sayarwa, da kuma irin matsalolin da suke fuskanta.
Waɗanne abubuwa ƙungiyarku ke gabatarwa a cikin watan Ramadan?
Mu kasance da ku a mako mai zuwa don samun amsar wannan tambayar da ma wasu tambayoyi da muke fatan za su amfani masu karatu.
