
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta umarci Majalisar Dattawa da ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Alƙalin a yayin hukunci, ta ce watanni shida na dakatarwa akan sanatar ya yi yawa, tana mai bayyana dokar tsayawa ta zango na 8 da sashe na 14 na iko da damanmaki na majalisa a matsayin masu tsauri.
Haka kuma, kotun ta umarci Natasha da ta bai wa majalisar haƙuri kan yin magana a wata kujerar da ba ita aka ware mata ba a yayin zaman majalisar.
Alƙali Nyako ta ƙara da cewa, duka majalisun dokokin biyu ba su iyakance adadin lokacin da dakataccen ɗan majalisa zai ɗauka ba kafin a sakar masa mara.
Takuma yi watsi da kalaman Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio na cewa kotun ba ta da ikon tsoma baki ko yin hukunci akan ƙarar duba da cewa abu ne na cikin majalisar.
Da farko, kotun ta umarci Natasha da ta biya tarar Naira miliyan 5 saboda bijire wa umarninta na hana yin magana akan lamarin da ya shafi ƙarar ga al’umma.
