A wani hukunci da ke tayar da ƙura a fagen ilimi da al’adu a Amurka, Kotun Koli ta ƙasar ta goyi bayan iyaye daga Jihar Maryland da ke ƙoƙarin hana ’ya’yansu halartar darussa da ke ɗauke da littattafai da ke tattauna batutuwan da suka shafi LGBTQ+, wato luwaɗi, maɗigo, da mutane masu sauyin jinsi.
Kotun ta yanke hukuncin da rinjayen ƙuri’u 6-3, inda ta ce iyayen da suka shigar da ƙara suna da ‘yancin samun kariya ta wucin gadi daga tilasta wa ’ya’yansu halartar darussan yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar gaba ɗaya.
Mai shari’a Samuel Alito, a cikin ra’ayinsa na hukuncin, ya bayyana cewa: “Gabatar da waɗannan littattafai ba tare da bayar da zaɓin ƙin halarta ba, ya haifar da nauyi na rashin ɗa’a kan ’yancin iyaye na gudanar da addininsu cikin walwala, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.”
Iyayen da suka shigar da ƙarar, waɗanda ke wakiltar addinai daban-daban, sun bayyana cewa, manhajar da makarantar Montgomery County ta gabatar tun shekarar 2022 tana saɓa wa aƙidunsu na addini, kuma hakan na tauye musu ’yancin zaɓar abin da ya dace da tarbiyyar ’ya’yansu.
Sun ce kundin tsarin mulkin Amurka, musamman sashi na farko (First Amendment) ya ba su ’yancin gudanar da addininsu cikin ’yanci, wanda ya haɗa da zaɓar darussan da suka dace da ’ya’yansu.
Sun ƙara da cewa, makarantar na bai wa iyaye damar hana manyan ɗalibai halartar darussan ilimin jima’i, don haka ya dace a ba su irin wannan dama a darussan da suka shafi zamantakewar LGBTQ.
Littattafan da aka ƙara cikin manhajar sun haɗa da ‘Uncle Bobby’s Wedding’, wanda ke labarin wata yarinya da aka sanar da ita game da bukin auren kawunta da wani namiji; da kuma ‘Born Ready: The True Story of a Boy Named Penelope’, wanda ke bayanin tarihin wani yaro mai sauyin jinsi.
Iyayen sun bayyana cewa ba su da wata matsala da kasancewar littattafan a cikin ɗakin karatu, amma suna so ne su kare ’ya’yansu daga karanta su a aji.
A cewar hukumar makarantar Montgomery County, wacce ita ce mafi girma a Maryland, an gabatar da littattafan ne don bunƙasa fahimtar al’umma da bambance-bambancen mutane. A shekarar 2023, makarantar ta dakatar da damar da iyaye ke da ita na fitar da ’ya’yansu daga darussan, tana mai cewa hakan na haddasa ruɗani a aji da kuma haifar da tsangwama ga ɗaliban da ke cikin al’ummar LGBTQ.
A ra’ayinta na adawa da hukuncin, Mai shari’a Sonia Sotomayor, ɗaya daga cikin alƙalan ra’ayin sauyi, ta ce: “Sakamakon wannan hukunci zai janyo ruɗani a makarantun gwamnati na ƙasar. Idan muka dubi yadda bambance-bambancen addini ke yawaita a Amurka, to babu makawa yara za su fuskanci darussa da ra’ayoyi da ke saɓa wa addininsu.”
Ita kuma shugabar ƙungiyar kare haƙƙin LGBT, Kelley Robinson, ta bayyana a wata sanarwa cewa: “Wannan hukunci ya aika da saƙon cewa, ɗalibai masu alaƙa da LGBTQ+ ba su da matsayi ko muhimmanci a cikin al’umma.”
Sai dai lauya Eric Baɗter, wanda ya wakilci iyayen a kotu, ya ce hukuncin “nasara ce ga dukkan iyaye a ko’ina.”
A wani zama na sauraron ƙarar a baya, alƙalan kotun sun bayyana rarrabuwar ra’ayi bisa akida, inda ɓangaren ra’ayin mazan jiya suka nuna goyon baya ga ƙorafin iyayen.
