A wata sabuwar rigima da ta kunno kai da ke ƙara rikitar da siyasar Thailand, kotun kundin tsarin mulki ta ƙasar ta dakatar da Firaminista Paetongtarn Shinawatra daga kan muƙaminta, biyo bayan yaɗuwar wani sautin tattaunawar wayarta da tsohon shugaban ƙasar Cambodia, Hun Sen.
A cikin wannan sautin da ya bayyana a kafafen sada zumunta, Paetongtarn ta kira Hun Sen da “kawu” tare da sukar wani babban hafsan soja na Thailand, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya a cikin al’umma tare da haddasa buƙatar a tsige ta daga kan kujerar mulki.
Kotun ta kaɗa ƙuri’ar dakatar da ita da rinjayen ƙuri’u 7-2, yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar tsige ta. Ta na da kwanaki 15 domin kare kanta gaban kotun. A halin yanzu dai, mataimakin firaminista zai ci gaba da riƙe ragamar shugabancin ƙasar na riƙon ƙwarya.
Sai dai, koda an dakatar da ita daga kujerar firaminista, Paetongtarn za ta ci gaba da zama a cikin majalisar ministoci a matsayin ministar al’adu, wani sabon muƙami da aka ba ta jim kaɗan kafin dakatarwar.
A ranar Talata, Paetongtarn ta sake bayar da haƙuri bisa abin da ya faru, tana mai cewa wayar da ta yi da Hun Sen “kashi ɗari cikin ɗari (100%) na kare muradun ƙasa ne.” Ta bayyana cewa tattaunawar da suka yi ta shafi rikicin iyaka da Cambodia, rikicin da ya daɗe yana faruwa amma ya sake ƙara zafi tun daga ƙarshen watan Mayu bayan kashe wani sojan Cambodia.
Sai dai ɓangarorin adawa musamman ‘yan siyasar ra’ayin mazan jiya sun zargi Paetongtarn da nuna sassauci ga Hun Sen da kuma rage darajar rundunar sojan Thailand.
A martaninta, ta ce: “Ban yi hakan don wata buƙata tawa ba. Na yi tunani ne kan yadda za a kauce wa rikici, a kauce wa faɗa, da kuma kare rayukan mutane. Idan aka saurari tattaunawar da kyau, za a gane babu wani mugun nufi a cikinta.”
Idan aka tabbatar da dakatarwar, Paetongtarn za ta zama mutum na uku daga cikin dangin Shinawatra, iyali da ke da ƙarfin faɗa aji a siyasar Thailand, da suka rasa kujerarsu kafin kammala wa’adin mulki. Kafin ta, danginta Yingluck Shinawatra da Thaksin Shinawatra (ubanta) duk sun fuskanci irin wannan makoma.
Tun makonni biyu da suka wuce, jam’iyyar da ke mulki ta fara fuskantar barazana bayan wata jam’iyyar kawance mai ra’ayin mazan jiya ta janye goyon bayanta, lamarin da ya rage yawan kujerun da ke sahun gwamnati.
A daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa, Thaksin Shinawatra, tsohon firaminista kuma uba ga Paetongtarn, na gaban shari’a kan zargin cin mutuncin masarautar Thailand, biyo bayan wata hira da ya yi da wata jaridar ƙasar Koriya shekaru tara da suka wuce. Shari’ar tasa ta fara ne a ranar Talata.
Thaksin, wanda ya dawo gida daga gudun hijira a shekarar 2023 bayan shafe shekaru 15 a waje, shi ne mutum mafi farin jini da aka taɓa gurfanarwa bisa dokar ‘lese majeste’, dokar da ta haramta sukar masarautar ƙasar.
Masana harkokin siyasa sun nuna damuwa game da irin tasirin da kotun tsarin mulkin ke da shi wajen rushe gwamnati. Tun daga shekarar 2006, kotun ta rusa jam’iyyu har guda 34, ciki har da jam’iyyar Move Forward mai akidar gyara, wadda ta lashe mafi yawan kujeru a zaɓen 2023 amma aka hana ta kafa gwamnati.
“Wannan ya zama tamkar al’ada a siyasar Thailand, wani ɓangare na al’adar siyasar ƙasar wanda ba haka tsarin dimokuraɗiyya ya kamata ya kasance ba,” inji Dakta Titipol Phakdeewanich, malamin kimiyyar siyasa daga jami’ar Ubon Ratchathani.
Paetongtarn, ‘yar shekara 38 da haihuwa, ita ce shugabar gwamnati mafi ƙarancin shekaru a tarihin ƙasar, kuma mace ta biyu da ta taɓa riƙe wannan muƙami bayan yayarta Yingluck Shinawatra. Amma da alamun matsin lamba da rikicin siyasa sun fara shafar farin jininta, yayin da rahotanni suka nuna cewa darajarta ta faɗi daga kashi 30.9% a watan Maris zuwa kashi 9.2% a ƙarshen mako da ya gabata.
