Yanzu-yanzu: Na hannun daman Kwankwaso, Hon. Abdulmumin Kofa ya koma APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Darakta Janar na ƙungiyoyin goyon bayan Tinubu, wato ‘Tinubu Support Groups’ kuma ɗan Majalisar Wakilai, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya fice daga Jam’iyyar NNPP inda ya koma mai mulki APC, yana mai bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu a zaɓen 2027.

Komawar ɗan majalisa APC ta nuna cewa jam’iyyar mai mulki ta samu gagarumar ci-gaba musamman a harkar siyasar jiharsa ta Kano.

Hon. Kofa ya sanar da haka ne a mahaifarsa ta Kofa da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji a jihar Kano, inda ya samu tarba daga dubunnan magoya baya da jagororin addini.

Aƙalla malamai guda 2,000 ne suka halarci taron inda suka gabatar da addu’o’in samun nasarori ga sabuwar alƙiblar siyasar ɗan majalisar da kuma nuna goyon bayansu ga samun nasarar Shugaba Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Haka kuma, sun yi addu’o’in neman zaman lafiya mai ɗorewa da ci-gaban mazaɓarsa ta Ƙiru/Bebeji da ma Nijeriya baki ɗaya.

Da yake jawabi a taron, Hon. Kofa ya bayyana farin cikinsa ganin yadda dubunnan al’umma suka nuna masa soyayya, yana mai fatan cigaba da hidimta musu a kowane mataki ya tsinci kansa.

By Babaji