
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro ƙarƙashin rundunar atisayen Haɗin Kai (OPHK) da na haɗaka a shiyyar Arewa ta Gabas sun yi gagarumar nasara a aikinsu na yaƙi da ta’addanci a jihar Borno.
A wata takarda da jami’in yaɗa labaran OPHK, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce jami’ai na musamman na Bataliya ta 135 a jiya Lahadi, sun yi artabu da mayaƙan Boko Haram/ISWAP a yankin Dutsen Kura a lokacin da suka gano cewa sun yi garkuwa da mutane a hanyar Buratai zuwa Kamuya.
A yayin farmakin ne sojojin suka yi nasarar kora mayaƙan zuwa yankin Mangari bayan nuna musu fin ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa mayaƙan tserewa daga yankin.
A lokacin da sojojin ke bincike a yankin, sun gano wasu maɓoyan ƴan ta’addan guda 11, sannan suka ceto mutane 86 waɗanda suka haɗa maza, mata da yara.
Haka kuma, sun ƙwato makamai ciki har da bindigar AK-47, mazubin alburusai guda biyar da alburusai 73 acikin su, kekunan hawa takwas, adaidaita sahu na kai kayan aiki biyu da sauransu.
Baya ga haka ne suka kuma tarwatsa sansanin mayaƙan.
A wani labari kuma, dakarun da aka tura aiki a Mangada, sun yi nasarar kama masu kai wa ƴan ta’adda kayan aiki su guda 29 a lokacin da suka nufi yankin Chilaria.
A yayin haka ne suka ƙwace motocin a kori kura guda biyu, adaidaita sahu cike da fetur da ya kai kimamin lita 1,000 acikin jarkoki, galan huɗu na baƙin mai, kayan abinci da dai sauransu.
