Yanzu-yanzu: Sarkin Zuru ya rasu a Landon

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan tsohon sojan kuma sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi.

A ranar 24 ga wata Oktoban shekarar 1943 ne aka haifi marigayi Sarki Sani Samiinda ya shiga aikin soja a 1962, ya kuma halarci makarantar horar da sojoji na Mons Officer Cadet School a Aldershot ta Birtaniya.

An kuma yaye shi a ranar 25 ga July, 1963 tare wasu ƴan ajinsu ciki har da tsohon shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB.

A zamanin mulkin Murtala Mohammed, marigayin ya yi aiki a matsayin kwamandan Birget ɗin sojoji a Legas.

Sannan bayan juyin mulkin da ya kai Janar Muhammadu Buhari mulkin a Disambar 1983, an naɗa shi gwamna a tsohuwar Jihar Bauchi har zuwa Agustan 1983.

Bayan ya yi ritaya a soja, ya koma ƙauyensa inda daga bisani aka naɗa shi a matsayin sarkin Masarautar Zuru a jihar Kebbi.

Ana tsammanin Masarautar Zuru ta sanar da lokacin jana’izarsa nan ba da jimawa ba.

By Babaji