Yanzu-yanzu: Tinubu na ganawar sirri da jagororin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A halin yanzu Shugaba Bola Tinubu na tattaunawar sirri da jagororin tsaro a Aso Rock da ke Birnin Tarayya Abuja.

Wannan shi ne karo na farko da shugaban ƙasar ke irin tattaunawar tun bayan rantsar da Janar Christopher Musa Gwabin a matsayin Ministan Tsaro a ranar 4 ga watan Disamba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗalibai 115 na makarantar kwana ta Catholic da ke Papiri a Jihar Neja ke cigaba da kasancewa a hannun ƴan bindiga tun bayan garkuwa da su a watan Nuwamba.

Idan za a tuna, a ranar 26 ga watan Nuwamba ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin tsaron Nijeriya inda ya umarci da ɗibi sababbin jami’an tsaro.

Haka kuma ya umarci a janye jami’an ƴan sanda daga gadin manyan mutane.

Ana wannan zama ne kwanaki kaɗan da Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu ta tura dakarun Nijeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin kifar da gwamnatin ƙasar.

By Babaji