Yadda Ali Nuhu maida ’yan Arewa saniyar ware a Hukumar NFC – Ƙungiyoyi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya a Kannywood (MOPPAN) da haɗin gwiwar ƙungiyar ’Yan Fim ta Arewa (AFMAN) sun nuna damuwa kan yadda ake ƙoƙarin mayar da su saniyar ware a harkokin Hukumar Kula da Finafinai ta ƙasa (NFC) tun bayan da Jarumi Ali Nuhu ya zama shugaban hukumar.

A wata wasiƙa zuwa ga shi Darakta Manaja na NFC, Ali Nuhu, wacce Shugaban MOPPAN fitaccen jarumi kuma shugaban MOPPAN na ƙasa, Shehu Hassan Kano da Shugaban AFMAN kuma fitaccen furodusa Salisu Mohammed Officer suka rattaɓa wa hannu, ƙungiyoyin sun bayyana damuwarsu bisa yadda ake nuna musu wariya da halin ko-in-kula da al’amuransu, daga ɓangaren wakilan NFC na Arewa.

Sun ce, gabanin daraktan ya kama aiki, hukumar tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta kiyaye aiki tare da ƙungiyoyin Arewacin Nijeriya ta yadda take bayar da gudunmuwa ga ci-gaban finafinansu, ayyukan al’adu, inganta matasa da haɗin kan ƙasa ta harkar fim.

Haka kuma, sun bayar da misali da taron bajekolin na ƙasa, wato Zuma International Film Festival, wanda NFC ta shirya na kwanan nan, wanda duk da cewa MOPPAN da AFMAN suna da muhimmanci da babbar rawa da suke takawa a kai, amma babu wata gayyata ko wakilci a hukumance na musamman da aka aika musu.

Sannan sun bayyana cewa, ci-gaban ƙasa ta ayyukan fasaha, musamman na masana’antun finafinai, za su samu ne yayin da aka samu haɗin gwiwa tsakanin dukkan ɓangarorin ƙasa da damawa da su ta yadda kowane ɓangare zai bayar da tasa gudunmawar.

Don haka suka yi kira ga ɓangaren da abin ya shafa da ya yi nazari akan al’amarin tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen warware matsalolin duba da yadda Kannywood, wacce ita ce masana’antar fim da ke kan gaba a arewacin Nijeriya wajen bayar da gagarumar gudumawa a fannin.

Kawo haɗa wannan rahoto dai, Hukumar NFC a ƙartƙashin jagorancin Ali Nuhu ba ta mayar da martani ba.

By ukarofi