
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana binciken da EFCC ke yi a kansa a matsayin abin da aka siyasantar, yana cewa lamarin ya samo asali ne bayan komawarsa jam’iyyar ADC.
A wani saƙo daga mai taimaka masa akan harkar yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, Malami ya zargi shugaban EFCC da yin aiki bisa ɗaukar ɓangare, yana mai tunatar da jama’a cewa Mai Shari’a Ayo Salami ta taɓa fitar da bayanai masu hujjoji masu ƙarfi akansa.
Saboda haka, Malami ya ce ba zai samu gaskiya da adalci ba a ƙarƙashin jagorancinsa yayin da yake cigaba da zama a hannunsu.
Saboda haka, Malami ya buƙaci shugaban na EFCC da ya janye hannu a lamarin tare da miƙa shi zuwa ga wata hukumar gwamnati da ta dace domin a dawo da sahihancin bin doka da oda.
Haka kuma, Malami ya nemi a gaggauta gurfanar da shi a gaban kotu ko a sakr shi kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, yana jaddada cewa kotu kaɗai ce ke da ikon yanke masa hukunci, ba hukumomin da siyasa ta rinjaya ba.
Kazalika, ya kuma soki ƙoƙarin amfani da mutanene da ke da laifi akansu daga waje a matsayin shaidu, yana cewa hakan suka ne ga tsarin bin sharuɗɗan doka.
A ƙarshe, Malami ya ce ba ya neman wata mafakar siyasa don don ci-gaban kansa, burinsa kawai shi ne ya wanke kansa a gaban kotu daga abinda ake tuhumar sa a kai.
