Yanzu-yanzu: Tinubu ya karrama ƴan wasan Super Falcons da Dala 100,000 da gidaje ga kowannensu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya karrama ƴan wasan ƙungiyar Super Falcons da kyutukan ƙasa, kuɗaɗe da kuma gidaje bisa nasarar lashe Kofin ƙasashen Afirka na mata (WAFCON) a karo na goma.

An gudanar da taron karramawar ne a Fadar Shugaban Ƙasar dake abun, ranar Litinin, inda baki ɗaya ƴan tawagar su guda 24 suka taru.

Shugaba Tinubu ya sanar da bai wa kowannensu kwatankwacin Dala 100,000 a kuɗin Naira da kuma gidaje masu dakunan bacci uku ga kowane mamba na tawagar.

Ya ce, ƴan wasan sun ƙara ɗaga darajar Nijeriya a idon duniya don haka ƙasa tana alfahari da su da ɗaukacin al’ummarta baki ɗaya.

A ranar Asabar ne Super Falcons ta Nijeriya ta lashe WAFCON a birnin Rabat na Ƙasar Moroko, bayan doke tawagar masu masauƙin baƙi da ci 3 da 2 a wasan ƙarshe.

By Babaji