Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar gyaran aƙida ta ƙasa ta fara rangadin faɗakar da jama’a mahimmancin yin allurar rigakafin cutar ƙyanda a ƙananan hukumomi 19 da ke jihar Katsina.
Daraktan hukumar a Katsina Malam Ibrahim Tsagem ya fitar da sanarwar hakan ga manema labarai a Katsina.
Ya ce waɗannan ƙananan hukumomi suna daga cikin waɗanda aka gano na iya kamuwa da cutar ta ƙyanda.
Tsagem ya bayyana ƙananan hukumomin da suka haɗa da Katsina, Kaita, Jibiya,Ɓatagarawa, Batsari, Safana,kankiya, Faskari.
Sai ƙanƙara, Sabuwa, Funtua da Musawa. Sauran sun haɗa da Rimi, Charanchi, Mani,Mashi, Daura,Ɓaure da Bindawa, a cewar daraktan.
Ya bayyana manufar rangadin faɗakarwar da yace zai ba mutane damar shirya wa a gudanar da allurar da za a fara a watan Oktoba cikin nasara.
“Faɗakarwar na da mahimmanci duba da yadda cutar ke nakasa jarirai da ƙananan yara, “cutar ƙyanda na kawo makanta, rashin ji har ya kai ga rasa rayukan yaran da mahaifiyar su ta kamu da cutar,”Daraktan ya faɗi haka.
Yara daga watanni 9 zuwa shekara 15 za ayi wa allurar riga Kafin a cewar shi.
Sai yayi kira ga iyaye da su tabbatar sun kai yaran su ayi masu allurar,ya ƙara da cewa allurar bai da wani lahani kuma kyauta ne.
