
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Ungozomomi ta Ƙasa (NANNM) ta bai wa Gwamnatin Tarayya kwanaki bakwai na ta inganta walwalarsu wajen samar da alawus mai auki da yanayin aiki mai kyau ga ungozomomi da mambobinta a faɗin Nijeriya.
Da fari, ƙungiyar ta ba gwamnatin wa’adin kwanaki 15 na ta amsa buƙatunda ta gabatar mata.
A sanarwar da Sakatariyarta, Enya Osinachi ta fitar daga Shugabarsu, Morakinyo Olajide Rilwan, ranar Litinin, ta ce an ɗauki matakin ne bayan zaman zaman kwamitin zartarwa da aka gudanar a ranar 10 ga Yuli a Abuja.
NANNM ta bayyana cewa hakan zai taimaka wajen gaggauta zama domin ɗaukar matakan da suak dace wajen warware matsalolin da suka gabatar wa gwamnati.
Za a shiga yajin aikin da misalin ƙarfe 12 na daren ranar Talata, 29 ga Yuli, inda za a tsayar da baki ɗaya ayyukan ungozomomin a asibitocin faɗin Nijeriya.
Ƙungiyar ta kuma kirayi ɗaukacin mambobinta da su bada haɗin-kai a yayin da aka fara yajin aikin.
