Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fatima Atiku Abubakar, ‘yar fari ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ta shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance.
An tarbi Fatima cikin jam’iyyar a ranar Litinin a Abuja.
Tsohuwar Kwamishinan Lafiya ta Jihar Adamawa ta yi rijista a hukumance a matsayin memba na ADC a gundumarta da ke yankin Wuse na Babban Birnin Tarayya, inda ta kuma karɓi katin zama memba na jam’iyyar.
Jami’an jam’iyyar da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun haɗa da Shugaban FCT na ADC, Clement Oba Ehigiator, shugaban Majalisar ƙaramar Hukumar Abuja ta jam’iyyar, da sauran manyan membobinta.
Fatima, a jawabinta, ta bayyana ADC a matsayin wani dandali da ke karɓar haɗin gwiwar ‘yan adawa da ke aiki don kawar da Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027.
Ficewarta ita ce ta baya-bayan nan a cikin jerin manyan ƙungiyoyi a cikin ADC, yayin da ‘yan adawa ke ci gaba da sake haɗuwa kafin zagayen zaɓe mai zuwa.
Ku tuna cewa tsohon ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, Sanata Abaribe da Aisha Yesufu suma sun koma jam’iyyar ADC kwanan nan.
