Daga SIDI KAZEEM
A kwanakin baya na yi wani rubutu game da yadda ƙananan yara ke yawo da sunan bara a birane da ƙauyukan ƙasarmu Nijeriya, musamman Arewa, inda na yi bayanin cewa, wannan abu ne da ya shafi duk wani mai kishin ’ya’yansa da cigaban al’umma.
A yau ma na sake juyawa kan wannan batu saboda muhimmancinsa, da kuma yadda ya zama jama’a suna wasa da wannan mummunan hali. Aikin jawo hankali ga iyaye, ko kuma kula da irin waɗannan yara aiki ne ya hau kan kowa. Wajibi ne duk mai wata kafa ta yin bayani, wa’azi ne, magana ce a kafafen yaɗa labarai, tsawatarwa ne da dai sauransu, mutum ya samu ya sauke nauyin da ke kansa, kamar dai yadda muke yi a wannan shafi.
Domin a gaskiya wannan abu ya zama wani bala’i ne, inda za ka ga yaro ƙarami yana bara, wanda zai iya yin duk wani aiki na ƙarfi, duk da kuwa a yanayi irin nasa, kamata ya yi a ce yana makaranta don neman ilimin da zai amfane shi duniyarsa da lahirarsa, amma abin takaici babu ko ɗaya, bai tafi makarantar Islamiyyar ba balle ta boko.
Wasu daga cikin waɗannan abubuwa, waɗanda kuma zan iya cewa babu wani mai farin ciki da shi, shi ne yadda za ka samu ƙananan yara masu ƙananan shekaru suna bara a kan tituna, musamman a wasu manyan garuruwan ƙasar nan, wasu kuma z aka tara da su a bola suna tsince-tsincen abubuwan da za su samu su sayar su sami kudi.
Irin waɗannan yara masu barace-barace suna nan birjik manya da ƙananan garuruwanmu, suna barar ta hanyoyi da dama, wasu suna tare da iyayensu ne kamar ’yan jagora, idan iyayen makafi ne, wasu kuma iyayen almajiran ne, don haka su ma suke cikin bara, wasu kuma almajirai ne da aka tura wasu garuruwan da ba nasu ba domin yin karatun allo. Amma yawancin masu tsince-tsince a bola din nan, daga gidajen iyayensu suke.
Irin waɗanan yara, wasu lokuta ma za ka tarar da cewa ƙanana ne matuƙa, ta yadda in da suna gidan iyayensu ne, kuma iayen suna san abin da suke, hatta wanki ko wanka ma sai an yi masu, wasu ma ba su wuce kwana da iyayensu mata a gado ɗaya ba.
To, amma abin takaici sai ya zama an raba su da iyayen nasu an jefa su bariki, wasu kuma iyayen nasu ne suka watsar da su, ba abin da suke yi sai bara, babu karatun addini balle na zamani. Su kuma waɗanda suke karatun allo daga cikinsu, yunwa da rashin ƙoshin kafiya ma ta ishe su. Idan suna cikin wannan yanayi, wa zai yi masu wanka, wa zai yi masu wanki da sauran hidindimu?
A duk lokacin da na ga ririn waɗannan yara na kan tausaya masu, kuma na kan tausaya wa iyayensu. Ina tausayin yaran ne bisa mummunan halin da aka jefa su na azabar rayuwa, sannan su kuma iyayen ina tausayinsu saboda wannan tamkar sun yi watsi da amanar da Allah ya ba su ne, kuma tabbas Allah zai tambayesu amanar da ya ba su a gobe kiyama.
Sannan wani abin ban tsoro a irin waɗannan yara ake turawa cikin wannan mummunan hali, shi ne gurɓatacciyar tarbiyyar da suke tashi da ita. Domin ba sa samun tarbiyya tagari, ba sa samun mai kwaɓa masu, irinsu ke tashi cikin mutanen nan masu aikata miyagun ayyuka.
Haka kuma irin waɗannan yara su suke tashi a ƙungiyoyin miyagun mutanen nan masu aikata miyagun ayyuka, ko kuma cikin waɗanda ake amfani da su wajen cimma munanan burace-burace na miyagun ’yan siyasar nan da ba sa ma kansu da al’ummarsu fatan alhairi.
Haka kuma a duk lokacin da aka samu wata hatsaniya, ta siyasa ce ta addini, to za ka tarar da irin waɗannan yara ne a sahun gaba wajen aiwatar da miyagun ayyuka. Su ne wajen kashe-kashen da ba hankali, sace-sacen kayan jama’a da ƙone masu dukiya, da dai sauran wasu munanan ayyuka.
A batun gaskiya irin waɗannan yara masu irin waɗannan shekaru kamata ya yi a ce suna zaune tare da iyayeynsu suna zuwa makarantar Islamiyya da ta boko. Domin shi karatu irin wannan, yaro na gaban iyayensa ma zai fi mayar da hankali, musamman domin yana samun kulawa.
Idan aka rinƙa kwasar irin waɗannan yara ana turasu wasu garuruwa da sunan wai karatun allo, to wane irin karatu ne waɗannan yara za su yi, waɗanda hatta abincin kirki bai ishesu ba? Ya ake son su yi rayuwarsu, ya ake ganin tasowarsu za ta kasance?
Idan duk aka je aka dawo za a taras da cewa waɗannan matsaloli ne da suka dabaibaye ƙasar Hausa, abin takaici! Kuma yawanci ana fakewa ne da addini, sai a ce wai yaro zai tafi neman ilimin addini, alhali ga yara nan suna haddace Alƙur’ani mai girma a gaban iyayensu, suna zuwa makaranta su dawo gidajensu ana lura da lafiya da tarbiyyarsu.
Shi kuwa wancan an tura shi wani gari an haɗa shi da wasu, ba uwa ba uba, Malaminsu, wanda shi kuma yaran sun yi masa yawa, wasu lokuta ma yaran kan faɗa cikin wani mawiyacin hali, ko ya kwashi wasu miyagun halaye, shi Malamin bai ma sani ba.
A matsayina na ɗan jarida na sha haɗuwa da irin waɗannan matsaloli da dama, na sha samun labarai masu baƙanta rai game da irin halayen da waɗannan yara kan shiga, wanda wasu labaran ma ba a iya yaɗasu saboda takaicin da ke ciki. Domin akwai wani lokaci da ake samun yanayin da ake kama irin waɗannan yara da aikata miyagun abubuwa, hatta luwaɗi.
Saboda haka ne nake ganin wannan aiki ne da ya rataya a wiyan kowa, musamman iyaye, gwamnati da shugabannin al’umma. Domin ita tarbiyya ta kowa da kowa ce, idan ta gyaru, to al’umma ce za ta ji daɗi, idan kuma ta lalace, to al’umma ce za ta kwashi kashinta a hannu.
Wasu Gwamnoni a jihohin Arewacin ƙasar nan, musamman jihar Kaduna da Kano sun yi yunƙurin hana waɗannan abubuwa, amma saboda rashin samun goyon bayan al’umma, abin yana neman gagara. Domin idan suka cika matsawa sai a ce Gwamna wane yana yaƙi da addini, wanda kuma abin sam ba haka yake ba. Addini daban, waɗannan abubuwa kuma daban.
Sannan kuma su waɗannan yara masu tsince-tsince a bola, shin iyayensu sun kasa kula da su ne, ko kuwa ba su damu da su ba ne ya sa suka bar su maimakon karatu sai suka ɓuge da tsince-tsince a bola? Domin a irin wannan yanayi, aka tarar da cewa magidanci ne zai bar gidansa tun da sanyin safiya, amma ba zai dawo ba sai bayan isha’i, bai san ci ko shan iyalansa nasa ba, balle tarbiyyarsu.
Ina so a yi mani kyakkyawar fahimta a nan, ba wai ina so ne in hana masu ra’ayin tattara yara don koya masu karatun allo ba ne, abin da nake nufi a nan shi ne, a samu yaran da suka san inda ke masu ciwo mana, waɗanda za su iya yi wa kansu hidindimu, waɗanda za su iya bambance damansu da hagunsu.
Zan rufe wannan rubutu nawa da yin kira ga Hukumomin da abin ya shafa, tare da sauran al’umma su dubi wannan lamari, don a san gyaran da za a yi don gyaran al’umma. Su kuma iyaye su sani ’ya’yan da Allah ya ba su, ya ba su ne amana, don haka zai tambayesu amanar da ya ba su.
Cikakken suna Kazeem shine, Sayyid Alkazeem M. Shareef Alhasan. Za a iya samun sa a wannan lamba waya 08062740226
