
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake cigaba da gudanar da zaɓukan 2026 a Ƙaramar Hukumar Birni a Abuja, jami’an tsaro sun kama wata mata ɗauke da tarin katinan zaɓe.
Blueprint.ng ta ruwaito cewa tuni jami’an suka yi ram da ita a rumfar zaɓe ta PU 001 da ke makarantar firamare ta Kabusa, EC 37/06/03/001.
An kama ta ne a lokacin da zaɓe ke gudana cikin lumana.
Saidai ba a kai ga kammala tantancewa ko kaɗa ƙuri’a ba a lokacin haɗa wannan rahoto.
