Za a gudanar da zaɓen 2027 lami lafiya — Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce za a gudanar da babban zaɓen 2027 cikin zaman lafiya da gaskiya, yana mai yi wa ’yan Nijeriya alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da hakan.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Jos, babban birnin Jihar Filato, inda ya buƙaci al’ummar jihar da su zaɓi dukkan ’yan takarar jam’iyyar APC.

Da yake magana kan zaman lafiya, Tinubu ya ce bai kamata bambancin harsuna, al’adu da addinai tsakanin ’yan Nijeriya ya zama sanadin rarrabuwar kawuna ba, illa ya zama abin da zai ƙara ƙarfafa haɗin kansu.

Ya ce: “An rasa rayuka da dama, an lalata dukiyoyi da kuma al’ummomi. Abin da muke gani a yau shi ne muhimmancin haɗin kai da daidaita bambance-bambancen da ke tsakaninmu.

“Mu duka ’yan uwan juna ne, Allah Maɗaukakin Sarki ɗaya ya halicce mu, sai dai muna magana da harsuna daban-daban. Amma magana da harsuna daban-daban ko kwana a ɗakuna daban-daban ba ya nufin cewa mu abokan gaba ne da juna.”

Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa na ƙara tura jami’an tsaro da ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakaninsu domin magance matsalolin tsaro.

Ya bayyana cewa jami’an tsaron daji 1,000 na samun horo, yayin da gwamnati ta sayo kyamarorin sa ido domin gano barazana tun da wuri.

Haka kuma, ya ce gwamnati na ƙoƙarin dawo da mutanen da rikice-rikice suka raba da muhallansu (IDPs) zuwa gidajensu domin su sake gina al’ummominsu.

Gangamin ya samu halartar gwamnonin jihohi, ministoci, jami’an APC, ’yan majalisar tarayya, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi.

By ukarofi

Leave a Reply