Za a iya cin tarar wanda bai yi inshorar mota ba Naira 250,000

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fara aiwatar da dokar tilasta mallakar inshorar motoci na Third-Party Insurance Policy a faɗin kasar tun daga ranar Asabar, 1 ga Fabrairu. Kwamishinonin ‘yan sanda a jihohi da dama kamar Legas, Kogi, Akwa Ibom da wasu sun bayyana cewa sun fara aiwatar da umarnin da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayar domin tabbatar da bin doka.

A jihar Legas, kakakin rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya buƙaci duk masu motoci da su tabbata suna da inshorar mota mai inganci domin gujewa hukunci. Haka kuma, a jihar Akwa Ibom, Kwamishinan ‘yan sanda Baba Azare ya jagoranci duba yadda ake bin dokar a birnin Uyo da Ikot Ekpene, inda ya bayyana cewa duk wanda ba shi da inshorar mota, za a ƙwace motarsa har sai ya bi doka.

A Edo, kakakin rundunar ‘yan sanda Moses Yamu ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sanda Betty Enekpen Isokpan Otimenyin ta buƙaci masu motoci su mallaki inshorar Third-Party domin kare duk wani mutum ko dukiya da zai samu rauni a hatsari. A Kogi kuwa, Kwamishinan ‘yan sanda Miller Dantawaye ya buƙaci dukkan matuƙan mota su tabbata sun bi doka domin gujewa hukunci.

A cewar sashe na 68 na dokar inshora ta 2003, duk wanda ya ƙi mallakar inshorar mota na Third-Party zai fuskanci hukunci mai tsanani, wanda ka iya kaiwa tara Naira 250,000 ko kuma zaman gidan yari na shekara guda ko duka biyun. Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa za a ci gaba da aiwatar da dokar har sai an samu cikakken bin doka daga masu motoci a faɗin ƙasar.

By ukarofi