Za a iya yin mummunar ambaliya a jihohi 13, inji NEMA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (wato NEMA) ta ce, jihohi 13 da al’ummomi 50, musamman a Arewa, akwai yiwuwar ganin an samu ruwan sama mai ƙarfin gaske, wanda zai haifar da ambaliya tsakanin 13 da 17 ga watan Satumba, 2023.

Mista Ibrahim Farinloye, ko’odinetan hukumar NEMA na yankin Legas ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Legas.

Farinloye ya lissafa jihohin da al’ummomin da suka haɗa da jihar Kano, inda al’ummomi irin su Sumaila da Ƙunchi za su iya shafa.

Ya kuma ce, Jihar Kebbi mai al’ummomi irin su Argungu, da Jihar Katsina a Bindawa, Jibiya, Kaita da Katsina za su shafa.

Sauran jihohin da ya ce, sun haɗa da Nijar tare da al’ummomin Kontagora, Mashegu, da New Bussa da kuma Jihar Kwara da kuma al’ummar Kosubosu.

“Jihar Zamfara, da al’ummomi irin su Ƙaura Namoda da Shinkafi; Jihar Bauchi, tare da Bajoga, Darazo, Kirfi, Azare, Jama‘are, Itas, Misau; Taraba, da Bali, Donga, Lau, Serti, Mutum-Biyu, Yorro, da kuma jihar Borno, da Briyel, Biu, Dikwa, Kukawa zai shafa,” inji shi.

Ya kuma ce Adamawa da Ganye, Mubi, Demsa, Jimeta, Mayo Belwa, Numan, Shelleng, Song, al’ummomi da Yobe, tare da Dapchi, Gashua, Geidam, Kanamma, Machina, Potiskum.

Jihar Gombe da Nafada da Jigawa, tare da Dutse, Gumel, Gwaram, Miga sauran jihohi da al’ummomin da kodinetan yankin ya ce lamarin zai shafa.

Farinloye ya qara da cewa, sakamakon ƙaruwar ruwan kogin Benue da Neja, an shawarci al’ummomin da ke kusa da kogunan biyu, har zuwa Bayelsa da su ɗauki matakan kariya nan da kwanaki masu zuwa.