Tabar wiwi: ‘Yan sandan Kebbi sun yi kamu mafi girma a tarihi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama manyan motoci guda biyu maƙare da tabar wiwi da ba a taɓa kama irinsa ba a tarihin tsaro a jihar ta Kebbi.

A motar ta farko mai lamba IT 21520 LA, Lagos, ’yan sanda sun kama surken ƙullin wiwi guda 4,927 da aka ƙiyasta kuɗinsa ya kai fiye da Naira miliyan 300. 

‘Yan sanda sun kama mutane uku masu suna Emmanuel Chukwuma ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Banden a Jihar Abiya, da Kanta Bisa ɗan Ƙaramar Hukumar Asaka a Ƙasar Ghana, tare da Ishola Adeyemi, ɗan Unguwar Alufon a Ƙaramar Hukumar Akure ta Jihar Ondo dangane da kayayyakin.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wata motar mai lamba IT 21608 LA, Lagos, maare da sulken ƙullin tabar wiwi guda 4,906. ’Yan sandan sun kama wani mai suna Abdulrazak Agboola ɗan asalin Unguwar Yana Ajiya a birnin Ibadan ɗauke da kayayyakin a cikin babbar motar.

An ƙiyasta cewa, jimillar ƙiyasin kuɗin sunƙin tabar wiwi da ‘yan sanda suka kama ya zarce Naira miliyan 600.

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa, an yi hayan direbobin motocin ne daga ƙasar Ghana domin su kawo tabar wiwi a kan kuɗi Naira 200,000 a mota ta farko yayin da aka yi alƙawarin biyan Naira 400,000 ga direban mota na biyu.

‘Yan sanda sun kuma kama albarushi Cartridges katon 30 wanda ke ɗauke da kwali goma a kowanne kuma akwai ƙwara 25 a ciki.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ya ce, sashen binciken manyan laifuka na rundunar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *