Tabbas Rasha za ta yi nasara a kan Ukraine – Kim Jong Un

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya ce Rasha na samun gagarumar nasara a faɗan da ta ke yi da maƙiya, kalaman da ke zuwa a ziyarar da shugaban ke ci gaba da gudanarwa a Moscow, a wani yunƙurin samar da kyakkyawar alaƙa ciki har da ta aikin soji tsakanin ƙasashen biyu.

Duk da cewa kawo yanzu babu wasu bayanai da ke tabbatar da cewa akwai wata yarjejeniya da ke bai wa Rasha damar samun makamai da kuma kayan aikin soji daga Korea ta Arewa, amma Amurka ta yi zargin cewa akwai yiyuwar ƙasar na shirin taimaka wa Moscow a yaƙin da ta ke yi da Ukraine.

Bayan isarshi a Rasha cikin jirgin ƙasa mai sulke, Shugaba Kim Jong Un ya yi musabaha da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a garin Vostotchny da ke matsayin babbar cibiyar harba tauraron ɗan adam a gabashin Ƙasar Rasha.

Shugabannin biyu sun tattauna har tsawo sa’o’i biyu, kafin daga bisani aka shriya wa shugaban na Koriya ta Arewa wata gagarumar liyafar cin abincin rana.

Kim Jong Un ya ce yana da yaƙinin cewa sojoji da kuma al’ummar Rasha, za su yi nasara a yaqin da suke yi da waɗanda ya kira su a matsayin masu nuna ɗagawa a wannan zamani.

Haka zalika, Kim ya kuma yi jinjina ta musamman ga sojojin Rasha saboda irin jarumtakar da su ke nunawa a fafatawar da suke yi da ƙasar ta Ukraine.

Wannan ne dai karo na farko da shugabannin biyu suka yi ganawa da juna tun bayan ganawarsu ta 2019, yayin da Amurka ke nuna fargabar cewa Korea ta Arewa za ta iya samar wa Rasha da muggan makamai don yaqar Ukraine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *