Za a riƙa yin sahihan zaɓuka a jagorancina, inji sabon Shugaban INEC, Amupitan

Spread the love

Sabon Shugaban Hukumar Zaɓe, Farfesa Joash Amupitan (SAN) ya yi alkawarin cewa a ƙarƙashin jagorancinsa za a riƙa shirya sahihi kuma karɓaɓen zaɓe a sassan ƙasar.

Da yake jawabi bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi, Farfesa Amupitan ya kuma ce a wa’adin jagorancinsa zai tabbatar da cewa wanda ya faɗi zaɓe ya taya wanda ya yi nasara murna, saboda ingancin zaɓen.

Ya ƙara da cewa zai yi aiki tare da sauran hukumomi, kamar hukumar bayar da katin ɗanƙasa (NIN), domin tabbatar da komai ya fi daidai.

“Babban burinmu shi ne yin sahihai kuma ingantattun zaɓuka da kowa zai amince da su ta yadda wanda ya yi rashin nasara sai ya kira wanda ya yi nasara da kansa domin taya shi murna”, kamar yadda ya shaida wa ƴan majalisar.

Amupitan ya maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin sabon shugaban hukumar ta INEC.

By Babaji