
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shirye-shirye sun yi nisa na auren ‘ya’ya guda tara na Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, waɗanda za a yi a rana guda a Abuja.
Al’amarin, wanda ba a saba ji ko ganin irinsa ba, ya haddasa cece-kucen al’umma musamman a lokacin da aka ga katin gayyatar auren na yawo a Soshiyal Mediya.
A ranar Asabar kafafen watsa labarai suka gano katin, wanda ke ɗauke da hoton Ministan da bayanai akan aurarrakin waɗanda za a yi su a Babban Masallacin Ƙasa da ke birnin tarayyar.
A cewar katin, za a gudanar da su ne a ranar 6 ga watan Fabarairu, 2026 da misalin ƙarfe 1:30 na rana a masallacin, wanda ɗaya ne daga cikin fitattun cibiyoyin ibada a Nijeriya.
Yara taran sune: Ibrahim, Suraj, Safiya, Maryam, Aisha, Fahad, Muh’d, Nana Firdausi da kuma Farida.
Da yake tabbatar da al’amarin, Kakakin jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Yusuf Idris ya shaida wa manema labarai ‘ya’yan sun haɗa da maza huɗu da mata biyar.
Ya bayyana cewa, za a gudanar da taron ɗaurin auren a babban masallacin Abujan a satin farko na watan Fabrairun, yana mai cewa tuni aka ƙaddamar da shirye-shirye domin tabbatar da yin hidimar cikin walwala.
Wannan al’amari ya haddasa cece-kuce acikin al’umma musamman a kafafen sada zumunta, inda da dama suke nuna mamaki yayin da wasu ke addu’o’i na gari da fatan alheri ga iyalan.
