‎Gwamna Raɗɗa ya nemi addu’o’in shehunnai a taron maulidin Inyass a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‎
‎Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wajen taron maulidin inda ya bayyana jin daɗin shi na kasancewar gagarumin bikin maulidin karo na 40 a garin Katsina.
‎
‎Manya-manyan mutane daga faɗin duniya suka halarci taron maulidin a inda wasu daga cikin suka gudanar da jawabai da addu’o’i daban daban.
‎
A cikin su akwai Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass daga kaolack ƙasar Senegal da Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi da manyan malamai da mabiya daga ƙasashe kaman su jamhuriyar Nijar, ƙasar Senegal, Mali da Kamaru.

Taron karo na 40 ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko inda aka ɗauki kwanaki bakwai ana gudanar da turuka na manyan malamai da mabiya domin ƙara zumunci da gudanar da addu’oi na samun zaman lafiya a ƙasa.

Gwamnatin Katsina sai da ta kafa kwamiti shirya taron ƙarƙashin mataimakin gwamnan Farouk Lawal Joɓe .

Ana sa ran mutane fiye da miliyan ɗaya suka halarci maulidin.

By ukarofi