Daga Rabiu Sanusi
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bai wa hukumar Hisbah umarnin daukar mataki kan wa su kungiyoyi da ake zargin da koyar da Luwaɗi da Maɗigo a Jihar Kano.
Umarnin na Gwamnan na zuwa ne bayan zargin ɓullar wasu ƙungiyoyi dake fakewa da tallafawa makarantu suna yaɗa mummunar dabi’ar auren jinsi a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar lahadin data gabata.
Tun da farko dai kwamishinan ya ce gwamnatin jihar baza ta amince da auren jinsi ba ko da akwai hakan a yarjejeniyar Samoa da ake zargin Najeriya ta sanyawa hannu.
“Na tattauna da mai girma Gwamna kuma ya nuna rashin jindadinsa da wannan yarjejeniya da aka ce ansa hannu idan ta tabbata hakan ne, kuma ya bada tabbacin wannan ba zai samu gurbin zama a jihar Kano ba, ya yi Alla-Wadai da shi saboda Kano gari ne wanda al’ummarsa kaso 98 cikin dari Musulmai ne, kuma Musulunci bai yarda da wannan ba”.
Dangane da batun ƙungiyoyin da ake zargi da yada aƙidun masu aikata Luwaɗi da Maɗigo, kwamishinan ya ce sun samu bayanai kan korafe korafen mutane kan lamarin.
”Wannan ma mun yi magana da shi(Gwamna) ya bai wa Hisbah umarni su je su zakulo su kuma duk inda aka samu irin wadannan za a dauki matakin da ya dace don baza mu yarda da a zo a gurbata mana al’ada da addinmun ba.
Daga karshe, kwamishinan ya ce ana tattaunawa da Malamai don zukulo dabarar da za a kaucewa fadawa wannan lamari a jihar
