
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Haɗakar jami’an tsaro a jihar Zamfara ta yi nasar ceto iyalan Sakataren Gwamnatin jihar, Malam Mohammed Abubakar Nakwada bayan shafe kusan sati biyu a hannun ƴan bindiga.
Sadiya Nakwada, A’isha Nakwada da Abubakar Ɗan Fulani ne waɗanda aka yi garkuwa da su a ranar 27 ga Yuli, 2025 a Gusau, babban birnin jihar.
Da ya ke tabbatar da lamarin, mai sharhi kan harkar magance matsalolin tsaro, Zagazola Makama ya ce an yi nasarar ceto mutanen ne a ƙarƙashin aikin haɗaka tsakanin jami’an ƴan sanda da wasu jami’an sirri daga hedikwatar rundunar a Abuja.
A wani rubutu da ya wallafa ta kafar sada zumunta, Makama ya bayyana cewa jami’an sun kai samame ne a maɓoyar ƴan bindigar bayan samun wani bayanin sirri akansa a yankin Ƙauyen Mareri da ke Gundumar Damba a Ƙaramar Hukumar Gusau.
Haka kuma, an kama mutanen biyar da ake zargin su da hannu a aikata laifin ba tare da harbin ko daya daga cikinsu ba, kamar yadda ya wallafa.
Mutanen sune; Hamza Umar, Abubakar Abdullahi, Aisha Umar, Mohammed Ibrahim, da Igeh Mohammed, waɗanda baki ɗayansu ƴan yankin Mareri ne, inda a yanzu suke hannun ƴan sanda yayin da ake gudanar da bincike akan su.
