Ogun: Jami’an EFCC sun kama ƴan yahoo a kusa da ɗakin karatun Obasanjo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, sun kai samame a ‘Green Legacy Hotel’ da ke cikin farfajiyar ɗakin karatu na ƙasa na Olusegun Obasanjo a Abeokuta, Babban Birnin Jihar Ogun.

A yayin haka ne aka kama wasu matasa bisa zargin su da ayyukan damfara ta intanet.

Saidai EFCC ba ta tabbatar da zancen ba a hukumance.

Matasa da dama jami’an suka kama da wasu motoci masu alfarma da kuma wasu ababe masu tsada, kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito.

An ruwaito cewa a safiyar ranar Lahadi ne jami’an suka ƙaddamar da atisayen a yayin wani ƙaramin taro a farfajiyar ɗakin karatun.

Darakta Manaja na ɗakin karatun, Vitalis Ortese ya tabbatar da aukuwar lamarin, saidai bai bada wani ƙarin bayani akan haka ba.

By Babaji