Wane ne Janar Murtala Ramat Mohammad?

Spread the love

An haifi Janar Murtala Ramat Mohammed ranar 8 ga watan Nuwambar shekarar 1938 a garin Kano, ya yi karatu a kwalejin Barewa da ke Zaria.

A shekarar 1959 ya shiga aikin soji, inda ya yi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy ta Sandhurst dake Birtaniya.

Janar Mutala ya samu muƙamin Laftanal a shekarar 1961.

Gabanin komawarsa Nijeriya a shekarar 1962, ya je rangaɗin aiki a ƙasar Congo a matsayin wani wakilin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar ɗinkin Duniya.

A shekarar 1964 ya ka bashi muƙamin Manjo na wucin gadi, bayan da aka bashi ragamar kula da sashin sadarwa a hedikwatar rundunar soji ta Kaduna.

Janar Murtala ya koma Legas inda ya zauna tare da kawunsa Alhaji Inuwa Wada a lokacin da aka ba shi Ministan Tsaro, kuma ya kasance a can har lokacin da aka yi juyin mulki na farko a shekarar 1966.

Shugaban ƙasa Manjo Jƙnar Aguiyi-Ironsi ya ƙara masa girma zuwa Laftanal Kanal koda ya ke shima na wucin gadi ne, a watan Afrailun shekarar 1966. Bayan juyin mulki na farko, sau uku Janar Murtala ke neman haɗa kan sojojin Arewa da ke Legas domin a yi juyin mulki na biyu, sai dai wannan yunƙuri bai yi nasara ba bisa harbe wasu sojoji da aka yi a Abeokuta.

Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yakin basasar da akai a shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman balle yankin Biafra daga Nijeriya.

A wannan lakacin Janar Murtala ya jagoranci rundunar sojin da suka murƙushe sojojin Biyafara tare da kawo ƙarshen yaƙi basasar baki ɗaya kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967.

Yana matsayin Birgediya ne sojojin da suka yi juyin mulki na uku a Nijeriya suka naɗa Murtala a matsayin shugaban ƙasa, inda a watan Janairun shekarar 1976 aka ƙara masa girma zuwa Janar mai anini huɗu, wato ƙololuwa kenan.

Har ila yau, a wannan lokaci ne Janar Murtala ya ƙirƙiro da sabbin jihohi bakwai, ya kuma bayyana buƙatar mayar da Babban Birnin Nijeriya zuwa Abuja da kuma alƙawarin miƙa mulki ga fararen hula a shekarar 1979.

To masu iya magana kan ce kana taka, Allah na nashi, ranar 13 ga watan Fabrerun sojoji ƙarƙashin jagorancin Dimka sukayi yunƙurin kifar da gwamnatin sa yunƙurin da bai nasara ba, illa dai kashe-kashen da aka yi, inda suka buɗewa motar Janar Murtala Ramat Muhammed wuta a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ofis.

Bayan mutuwarsa an naɗa mataimakinsa laftanar Janar Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa.

By ukarofi