Wata nakasasshiyar mata mai suna Rita Idehen, ‘yar shekara 36, ta samu hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari saboda samun ta da laifin mallakar tabar wiwi mai nauyin kilogiram 2.5, Loud kilogiram 1.8 da Swinol kilogiram 2.2.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Benin a jihar Edo ta yanke wa mai laifin hukuncin ɗaurin rai da rai, bayan an same ta da laifuffuka biyu masu lamba: FHC/B/114C/2022, kuma Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta ƙasa NDLEA ta kafa.
Mai Shari’a Chuka A. Obiozor da Mai Shari’a J. B. O. ƙuadiri ne suka yanke hukuncin.
Sai dai kotun ta danƙa wa mai laifin zaɓin biyan tarar Naira Miliyan uku.
Hakazalika, hukumar ta NDLEA ta kuma samu hukuncin ɗaurin rai da rai ga wasu mutane shida bisa laifukan da suka shafi muggan ƙwayoyi a cikin watan Yulin 2025.
