Zamfara: ‘Yan bindiga sun halaka mataimakin ciyaman da awon-gaba da masu shayarwa biyar bayan karɓar miliyan N15

Spread the love

Al’umma a Jihar Zamfara sun tsinci kansu cikin yanayi na alhini da jimami bayan samun labarin kisan gilla da ‘yan bindiga suka yi wa Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Bukuyum, Honarabul Mu’azu Muhammad Gwashi.

Rahotanni sun bayyana cewa, marigayin ya shafe tsawon watanni shida a tsare a hannun maharan kafin su halaka shi.

Bayanai masu ratsa zuciya sun nuna cewa ‘yan bindigar sun riga sun karɓi kuɗin fansa har Naira miliyan 15 daga hannun iyalansa da nufin za su sake shi, amma suka yi ƙememe suka kashe shi duk da biyan kudin.

Wannan ɗanyen aiki ya kara jefa fargaba a zukatan al’ummar yankin, yayin da ake cigaba da addu’ar Allah ya jikansa da rahama.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Mahmud Muhammad Ɗantawasa, ya miƙa ta’aziyyarsu ga iyalai da al’ummar Bukuyum bisa abin alhinin.

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun farmaki al’ummar ƙauyen Saran Wawa da ke Gundumar Ruwan Rana inda suka yi awon-gaba da masu shayarwa guda biyar da wasu mutane huɗu.

Wani makusancin waɗanda abin ya shafa mai suna Malam Shehu ya ce al’amarin ya faru ne da tsakar dare a ranar 8 ga watan Disamba.

By Babaji