Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da sabon tsarin gwamnati a yanar gizo (E-Governance)

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ƙaddamar da sabon tsarin Gwamnati a yanar gizo (E-Governance) ga manyan sakatarori da daraktoci a ma’aikatun gwamnati (MDAs), a mataki na inganta aiki ga jama’a a jihar.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar da aka gudanar a KATDICT, Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan mataki a matsayin “babbar tarihi a tafiyarmu ta kafa gwamnati ta zamani, mai inganci kuma mai mayar da hankali kan ‘yan ƙasa a Katsina.”Inji Dikko.

Ya ce wannan shi ne mataki na farko na shirin gwamnati marar takarda, “gyaran da aka tsara don sauya yadda hukumominmu ke aiki, mu’amala da kuma isar da ayyuka.”

“Burinmu mai sauƙi ne amma mai muhimmanci da kawo zamanin dijital da zai kawar da tsofaffin tsarin takardu masu jinkirta aiki,”ya ce.

Dikko Raɗɗa yace wannan sabon tsari zai sanya hidimar gwamnati wacce ke da sauri, basira, tsafta kuma mai gaskiya—gwamnati da ta dace da buƙatun tattalin arzikin ƙarni na 21,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wannan sauyi ba abin da ya faru haka kawai ba ne. “Sakamakon zuba jari ne da muka yi don ƙarfafa tsarin dijital.” Ya ce ta hukumar wutar lantarki da makamashi, ofisoshin gwamnati yanzu suna samun wutar lantarki mai ɗorewa domin tsarin dijital ba zai yi tasiri ba ba tare da wuta tabbatacciya ba.

Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa an faɗaɗa layin intanet mai saurin gaske zuwa dukkan MDAs.

“Yau, dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomi suna da damar da ba su taɓa samu ba na intanet mai sauri. Wannan shi ne ginshikin gwamnatin dijital,” in ji shi.

Ya bayyana yadda aka ƙarfafa kayan aikin ICT, dawo da martabar KSITM da hukumar ICT ta jihar, tare da ba wa ma’aikata horo sosai.

By ukarofi