Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke jihar Katsina a Nijeriya ya ce zai amsa gayyatar da majalisar wakilan ƙasar ta yi masa bayan wani ma’aikacin jami’ar ya kai ƙararsa gabanta.
Kazalika, Farfesa Armayau Hamisu Bichi ya musanta zargin “rashin iya jagoranci” da mutumin mai suna Shehu Abubakar Tadda ya zarge shi, yana mai cewa ba shi ne ya kore shi daga aiki ba.
“Majalisar zartarwa ta jami’a ta kore shi daga aiki ne bayan wani kwamati ya gayyace shi ya je ya kare kansa kan wani rubutu da ya yi inda a ciki ya zagi ministan ilimi, shi kuma ya ƙi zuwa,” kamar yadda farfesan ya shaida wa BBC.
“Sai shi kuma yake yawo yana cewa ni ne na kore shi daga aiki. Ni ban isa na kori kowa daga aiki ba. ɗauka da kora daga aiki aikin majalisar jami’a ne, amma zan je majalisa [ta wakilai] domin na yi musu bayani.”
Wani kwamatin majalisar wakilai ya buƙaci shugaban jami’ar ya bayyana a gabansa ranar Laraba, 18 ga watan Satumban 2024. Majalisar ta kuma buƙaci wanda ya shigar da korafin ya bayyana gabanta.
Majalisar wakilan ta ce sashe na 88 da 89 na kundin mulkin Nijeriya ne suka ba ta damar gudanar da bincike kan batutuwa da suka shafi al’ummar ƙasar.
