
Majalisar Shura ta jihar Kano ta gayyaci shehin malamin nan da ake zargi da furta kalaman ‘ɓatanci’ ga janibin Annabi Muhammad SAW a birnin Kano, wato Sheikh Lawal Abubakar Shu’aibu Triumph da ya je gabanta domin kare kansa.
Sakataren Majalisar, Shehu Wada Sagagi ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yamamcin yau Laraba a birnin Kano.
Ya kuma ƙara da cewa, Majalisar ta dakatar da malamin daga tattauna batun da ake zarginsa da shi wanda ya janyo cece-kuce har zuwa lokacin kammala bincike bayan karɓar bahasinsa.
“Ba wai shi kaɗai Majalisar ta dakatar daga tattauna batun da ya janyo ruɗani har ma da dukkannin sauran malamai da al’ummar gari. Muna kira da a kame daga tattauna batun a jira har sai sakamakon binciken ya fito.” Inji Sagagi.
Tun bayan da wani ɓangare na al’ummar jihar suka gudanar da zanga-zangar lumana zuwa gidan gwamnati bisa zargin Sheikh Triumph da yin ‘kalaman ɓatanci’ ga janibin fiyayyen halitta, al’amura a Kano suka rincaɓe, kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.
