Zargin ɗaukar nauyin ’yan bindiga: Kungiyar Birnin-Gwari ta caccaki El-Rufa’i

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

wata ƙungiyar ta masu goyon bayan shugabanci na gari a Birnin-Gwari, wato ‘Birnin-Gwari ɓanguard for Security and Good Goɓernance’, ta yi tir da abinda ta kira da kalaman ƙarairayi da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya ƙirƙira akan tsarin zaman lafiya na Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari a jihar.

Ta bayyana kalaman nasa a matsayin ‘kare mai haushi ga wata’ duba da cewa sun ci karo da abinda ya bayyana a zahiri ga al’umma a yankin.

A wata takarda da Shugaban ƙungiyar, Ibrahim Abubakar NaGwari ya fitar, ƙungiyar ta bayyana kalaman El-Rufa’i na cewa Gwmanatin jihar da Mai ba Shugaban ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA) sun biya ’yan bindiga wasu kuɗaɗe a matsayin ɓangare na sharaɗin ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da su.

Ta ce, furta hakan da El-Rufa’i ya yi ƙoƙari ne na lulluɓe nasarorin da aka samu a sanadiyyar shirin dawo da zaman lafiya a ƙaramar hukumar.

Haka kuma ta ce, garuruwan da ke ƙaramar hukumar ne suka samar da shirin zaman lafiyar da kansu ta hannun masarauta da haɗin-gwiwar gwamnan jihar da ofishin NSA.

Kazalika, ta tabbatar da cewa babu wani kuɗi da aka biya ’yan bindigar yayin da suka ajiye makamansu

Buƙatun da bindigar suka gabatar a matsayin sharuɗɗan yarjejeniyar sune: buɗe kasuwannin dabbobi, barin al’ummarsu su riƙa yawo ba tare da tsangwamarsu ba, samar musu da cibiyoyin lafiya, samar da makarantu da famfunan ruwa na zamani, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

By ukarofi