Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungiyar Malaman Kwalejoji ta Nijeriya (COEASU), ƙarƙashin shugabancin reshan ta na makarantar sha re karatun jamia da karatu mai zirfi da aka fi sani da ‘Kano State College of Education Preliminary Studies’ ƙarƙashin shugabancin Dakta Sunusi Yakubu Ahmad Bichi da kwalejin da ya ke shugabanta ta karɓi taron ƙungiyar a wannan karan wanda kuma shugaban wannan ƙungiya na makarantar da akafi ta CAS kwamaret Aminu Hamisu Auwalu ya jogranci wannan gagarunmin taron na COEASU na Arewa Maso Yamma wanda ya gudana a birnin Kano wanda aka fara a ranar litinin da ta gabata.
A jawabin sa shugaban ƙungiyar COEASU na CAS kuma shugaban taron ya bayyana cewa wannan taro sun gamsu da yadda wannan taro kwaliya ta biya kuɗin sabulu domin kuwa an samu shugabanin wannan ƙungiya sama da 16 da suka halarci wannan taro wanda ya kasance na jahohin Arewa maso yamma kuma an tattauna mahimman abubuwa wanda zasu kawowa ƙungiyar da makarantu su cigaba mara iyaka wannan ba ƙaramin nasara ba ce a cewar shugaban wannan ƙungiya na CAS kuma jagoran taron ƙungiyar na Arewa Maso Yamma da Kano kuma CAS da haɗin kan shugaban Kwalejin mataimakin Farfesa Dakta Sunusi Yakubu Ahmad Bichi abin a yaba ne ga ɗaukacin jamian gudanarwa da sauran masu ruwa da tsaki na wannan kwaleji ta CAS da ke Kano.
A ƙarshe Kwamarade Aminu Hamisu Auwalu ya yabawa gwamnatin Kano Kan irin kyakyawan haɗin kai da gudunmawa da ƙungiyar ke samu wajen zaman lafiya da kuma mutunta juna a tsakanin ƙungiya da hukumar makaranta da sauransu wanda kuma hakan ce tasa mataimakin gwamnan Kano Kwamarade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilci gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wannan abun farin ciki ne kwarai da gaske.
