Ba da igiyar auren wani na shigo harkar fim ba – Aisha Muhammad (Momi)

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU

An daɗe ana samun matsalar shigowar matan aure harkar fim ta hanyoyi da dama ba tare da an san da hakan ba sai kuma daga baya idan ta bayyana matar aure ce abin ya kan karewa da rigima ko kuma a dangana zuwa ga hukuma. 

Akwai misalai da yawa da hakan ta faru, amma babban misalin da ya fi shahara shi ne na baƙuwar Rarara da aka yi a shekarun baya, lokacin da wata matar soja ta zo aka saka ta a fim sai bayan an zo an kwashi su Dauda Rarara da Usman Mu’azu a motar sojoji ta bayyana ai matar aure ce da tafe daga gidan soja ta shigo harkar fim. Duk wanda ya saurari waƙar Rarara a lokacin ta ‘Bakuwar Rarara’ ya san sun gamu da gamon su.

Ko a ‘yan kwanakin nan an samu wani labari na wata sabuwar jaruma mai suna Aisha Muhammad Momi da ta shigo harkar fim da aka yi mata zargin ta shigo harkar fim ne da igiyar auren a kanta.

A lokacin da muka yi magana da Aisha Muhammad Momi ta ce ” Gaskiya wannan labarin da ake yaɗa wa a kaina ba gaskiya ba ne, domin ni ba da aure na shigo harkar fim ba, kawai dai wani ne nake ganin ya ƙirƙiri labarin domin ya ɓata mini suna. 

Abin da na sani shi ne, mun yi aure da mijina kuma mun rabu da shi bayan wata shida da yin auren mu don haka babu yadda za a ce da aure na shigo harkar fim. Don har shaidar takardar sakin ma ina da ita, don haka ni ba da aure na shigo harkar fim ba, duk labarin da ake yaɗa wa a kaina ba gaskiya ba ne.”

Aisha wacce ‘yar asalin Jihar Yobe ce ta ce shi wannan mijin da ta aura daman tun kafin su yi aure ta faɗa masa tana da sha’awa ta yin fim don haka ba ta ɓoye masa ba. Kuma daga baya suka rabu ta dawo Kano ta ci gaba da yin harkar fim, don haka ba matar aure ba ce.

Da muka tambaye ta ko shi ne mijin ta na farko?

Ta shaida mana cewar ba shi ne mijin ta na farko ba, ta yi aure tun a baya har ma ta na da yara biyu da tsohon mijin nata.

By ukarofi