Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban mulkin sojin Nijar, Birgediya Janar Abdurrahamane Tchiani, ya zargi Nijeriya da Faransa da kitsa yunƙurin afka wa ƙasarsa ko yi wa Nijar bi-ta-da-ƙulli.
Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na ƙasar, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi zargin cewa, Faransa ta yi alƙawarin bai wa Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu wasu kuɗaɗe don kafa sansannin soji a dajin Baga da ke Jihar Borno, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Nijar.
“Akwai kuɗin da suka ce za su bai wa Tinubu domin ya ba su wani wuri cikin dajin Baga a jihar Borno, wani wuri da Turawan suka yi wa laƙabi da ‘Canada’, inda suke horas da al’umomin da waɗannan yankuna,” inji Janar Tchiani.
A cikin hirar mai tsawon sa’a guda da rabi, shugaban mulkin sojin na Nijar, Janar Tchiani ya zargi Faransa da ƙulla ƙawance da wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin Tafkin Chadi domin yi wa tsaron ƙasar Nijar zagon-ƙasa.
”Faransa ta ƙulla ƙawance da mayaƙan ISWAP da Boko Haram domin horas da su da ba su makamai da kuɗaɗe domin ta yi amfani da su wajen tayar da zaune-tsaye a Jamhuriyar Nijar,” inji shi.
Shugaban na mulkin sojin Nijar ya ce daga bayanan da suka samu a daɗewa sun fahimci cewa na shirin kafa sansanin Lakurawa a wani daji da ke jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Kebbi.
”Wasu manyan ‘yan ta’adda da muka kama, sun shaida mana cewa a ranar 4 ga watan Maris ɗin shekarar 2024, Faransa ta ƙulla wata yarjejeniya da mayaƙan ISWAP, kuma shugabannin Nijeriya na sane da ita, cewa za a mayar da dajin Gaba da ke jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi a Nijeriya sansanin horas da mayaƙan Lakurawa,” inji shugaban na Nijar.
Janar Tchiani ya yi zargin cewa an tanadin sansanin ne domin horas da mayaƙan Lakura don su watsu a jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma jihar Kebbi da kuma jamhuriyar Nijar.
Shugaban na Nijar ya ce duk da iƙirarin mayaƙan da suka kama suka na cewa jagororin Nijeriya na sane, ba su yarda da maganar ‘yan bindigar ba.
”Kan haka ne muka yanke shawarar bai wa Nijeriya waɗannan bayanai, saboda ba mu yarda da jawaban na ‘yan bindigar ba, muka faɗa wa shugaban hukumar leƙen asiri ta NIA na wancan lokaci da Ahmad Rufai Abubakar, ya turo mutane cikin Nijar domin tattaunawa da ‘yan ta’addar domin tabbatar wa daga bakinsu.”
Amma daga ƙarshe a cewar shugaban Nijar, sun gwammace ba su faɗa masa wannan sirri ba, indasuka zarge shi da ɗaukar nauyin horas da ‘yan ta’adda.
”Ashe shi wannan Ahmad Rufai Abubakar da muka shaida wa wannan sirri, shi ne ke ɗaukar nauyin tura ‘yan ta’adda zuwa wata ƙasa da ake kira Central Africa domin samun horo,” inji shi.
Haka ma shugaban na Nijar ya zargi mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da masaniya game da wannan batu.
”Duk sun san da zancen, amma suka yi shiru, tun daga nan ne muka fahimci cewa kifi tun ga kai nai ya ruɓe.”
Yayin zargin cewa an ƙuduri aniyar horas da Lakurawan ne domin su kawo tarnaƙi ga aikin bututun man ƙasar da ka shimfiɗa zuwa Jamhuriyar Benin mai makwabtaka.
Janar Tchiani ya zargi ƙasashe makwabtan Nijar da bai wa Faransa damar kafa sansanoni a ƙasashen domin horas da ‘yan ta’adda da niyyar yaƙar Nijar.
A baya-bayan nan dai dangantaka tsakanin Nijeriya da Nijar na ci gaba da yin tsami, ko a makon da ya gabata ma gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta zargi Nijeriya da shirya mata maƙarƙashiya, kodayake gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin.
Sai dai gwamnatin Nijeriya ta musanta duka zarge-zargen na shugaban mulkin sojin na Nijar.
Cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya fitar ya ce Nijeriya ba ta taɓa ƙulla wata alaƙar soji da Faransa ko wata ƙasa domin ɗaukar nauyin hare-haren ta’addanci a Jamhuriyar ta Nijar, ko tayar da zaune-tsaye a ƙasar.
Mohammed Idris ya ce shugaban Nijerya Bola Tinubu a matsayinsa na shugaban Ecowas yana gudanar da jagoranci da ya kira ‘abin koyi’.
”Kuma Nijeriya na iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da ɗorewar danganta mai tarihi tsakaninta da Jamhuriyar Nijar,” inji Ministan.
Ministan yaɗa labaran na Nijeriya ya ce dakarun ƙasar, tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasashen da ke yaƙi a Tafkin Chadi na samun nasara a yaƙin da suke yi da ‘yan ta’adda a yankin.
”Don haka hikima wani ya yi zargin cewa Nijeriya za ta haɗa baki da wata ƙasar waje domin wargaza zaman lafiya da tsaron makwabciyarta,” inji sanarwar.
Dangane da zargin wasu jami’an gwamnatin Nijeriya da Janar Tchiani na cewa suna ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda da ba su horo kuwa, ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce babu ƙamshin gaskiya game da zargin.
”Gwamnatin Nijeriya ko wani jami’inta ba su taɓa sanya hannu a bai wa ‘yan ta’adda tallafin makamai domin kai wa Nijar hari,” inji shi.
Haka kuma ministan ya musanta zargin bai wa Faransa wuri domin kafa sansanin.
”Nijeriya ba ta taɓa bai wa wata ƙasar waje damar kafa sansanin soji a ƙasarta ba”.
Nijar ta yi zargin ana shiryo mata maƙarƙashiya daga Nijeriya
Haka kuma ministan ya musanta zargin da shugaban na Nijar ya yi wa Nijeriya na yi wa bututun manta da harkokin noman ƙasar zagon-ƙasa.
Mohammad Idris ya ce Nijeriya ta riƙa gudanar da abubuwa na tallafa wa tattalin arzikin Nijar ta hanyar shirye-shiryen samar da makamashi, kamar shimfiɗa bututu iskar gas, na ‘Trans-Saharan Gas Pipeline’ da shimfiɗa layin dogo daga Kano zuwa Maraɗi.
”Babu hikima mutum ya yi tunanin cewa Nijeriya na yi abin da zai durƙusar da tattalin arzikin Nijar.”
Kan batun zargin haɗin bakin Nijeriya da Faransa wajen kafa cibiyar Lakurawa a jihar Sakkwato, ministan ya ce zargi ne maras tushe.
”Nijeriya ta kasance ja gaba a yaƙi da ta’addanci, inda take sadaukar da kuɗaɗe masu yawa da rayukan jami’anta domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi”, inji Mohammed Idris.
Za mu yi bincike – Majalisar Dattawa
A nata ɓangare majalisar dattawan ƙasar, wadda yanzu haka ke hutu, ta alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan waɗannan zage-zarge, da zarar ta koma baikin aiki.
Babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Tahir Munguno – wanda ke wakiltar arewacin Borno, ya ce ya kaɗu da waɗannan manyan zarge-zarge da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi kan gwamnatin Nijeriya.
Cikin zantawarsa da BBC, Sanata Munguno ya ce bisa tsarin dokokin Nijeriya dole idan za a kawo sansanin sojin wata ƙasa zuwa Nijeriya, to dole ne sai an nemi sahalewar majalisar dattawan ƙasar.
”Amma mu daga ɓangarenmu har yanzu, babu wata buƙata mai kama da haka da shugaban ƙasa ya aiko mana majalisa,” inji shi.
Amma ya ce da zarar majalisar ta ƙare hutunta za ta gudanar da bincike kan wannan batu.
”Za mu gayyaci ministan tsaro da babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar, mu ji gaskiyar wannan zargi,” inji shi.
