Rundunar ‘yan sandan Kano ta yi nasarar gano mashinan adaidaita sahu da aka sace

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Salman Dogo Garba ta yi nasarar gano wa su mashinan adaidaita sahu guda biyu tare da miƙa su ga asalin masu su.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’ar nan.

Sanarwar tace gano ababen hawan guda biyu na da nasaba da haɗa wata tawaga na masu binciken sirri daga cikin jami’an rundunar tasu a wani ɓoyayen guri da ke Ƙaramar hukumar Ɗambatta da ɓarayin suke a ranar tara ga wannan wata na Disamba.

Sanarwar tace masu Kekunan adaidaita sahun su bayyana a hedikwatar ‘yan sanda dake Bampai tare da bada dukkan shaidar da ta tabbatar suke da mallakin kayan su.

”Mashin na farko dake ɗauke da Lambar rajista kamar haka KGM 246VC an sace shi ne bayan yin kokawa tare da yima mai mashin din mai suna Mamman Musa rauni da makami.

Kiyawa yace yanzu haka mai mashin ɗin an kwantar dashi a asibitin Murtala inda yayi jinya daga bisani aka sallame shi bayan samun lafiya.

”Sai na biyun ma anyi amfani da hanya iri ɗaya da ta farko wajen ƙwatar shi inda mashin din yake ɗauke da Lambar rajista kamar haka KMC 319 VK,wanda haka mai shi Sani Ismail yazo ya bada dukkan hujjojin daya kamata su tabbatar nashi ne.

Kiyawa cikin sanarwar yace waɗanda ake zargi da satar adaidaita sahun masu suna Ado Yusuf mai shekaru40 da Rabiu Suleiman mai shekaru 35 da sayen mashinan wanda yanzu haka kuma an tasa ƙeyar su zuwa Kotun Majistire mai lamba 45 dake Gyadi-Gyaɗi dan cigaba da gudanar da bincike.

Daga Ƙarshen sanarwar tace kwamishinan ‘yan sandan na Kano CP Salman Dogo ya gargaɗi masu tuƙa adaidaita sahu wajen sanin irin fasinjojin da zasu ɗauka.

Dogo Garba ya kuma buƙaci al’umma dasu rinƙa isar da koken su ga jami’an ‘yan sanda domin ɗaukar matakin da ya kamata.

By ukarofi