Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Dakarun runduna ta 1 da haɗin-gwiwar ta 2 dake Arewa maso Yamma na atisayen ‘Fansan Yamma’ sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama, tare da hallaka wani ƙasurgumin ɗan ta’adda da aka fi sani da Alhaji Ma’oli.

Kodinetan yaɗa labaran dakarun, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau yau Juma’a.

Acewar sanarwar, rundunar ta kai samamen ne a ranar Alhamis a ƙauyen Mai Sheƙa dake kusa da garin Kunchin Kalgo, wanda ɗaya ne daga cikin yankunan da suka sha fama da ta’addanci a ƙarƙashin mulkin Ma’oli.

Sanarwar ta bayyana cewa, Ma’oli ya yi suna a kullum wajen sanya harajin da ba bisa ƙa’ida ba ga mazauna Unguwan Rogo, Mai Sheƙa, Magazawa, da sauran yankunan dake kusa da Bilbis a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, kawar da Ma’oli ya kawo farin ciki ga mazauna yankin Bilbis dake yammacin ƙaramar hukumar.

Laftanal Abubakar ya ce an fara aikin ne a matsayin martani ga rahotannin sirri na ‘yan ta’adda dake gudanar da ayyukansu a ƙauyen Bilbis.

“Martanin da sojojin Operation Fansan Yamma suka yi, ba wai kawai ya daƙile shirin ‘yan ta’addan ba ne, har ma mun ƙara dagewa wajen tabbatar da tsaro a yankin dake fuskantar tashe-tashen hankula a sakamakon ayyukan ƴan ta’adda.”

Ya kuma bayyana cewa rundunar ‘Operation Fansan Yamma’ za ta cigaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan ta na kakkaɓe sauran ‘yan ta’addar haɗin-gwiwa da Theater of Operation,” inji shi.

By Babaji