Zargin badaƙalar N6.5bn: ‘Yan sanda sun kama ɗan jaridar Kano bisa ƙorafin mataimaki ga Gwamna Abba

Spread the love

A ranar Asabar Rundunar ƴan sanda reshen Zone 1 Kano, ta kama tare da tsare ɗan jarida Ibrahim Ishaq, wanda aka fi sani da Ɗan’uwa Rano.

Jami’an sun kama sanannen ɗan jaridar mai gabatar da shirye-shirye kuma shugaban sashin shirye shirye na musamman na Hikima Radio Ibrahim Ishaq ne inda suka yi masa tambayoyi bisa zargin ɓatanci.

Hakan ya biyo bayan ƙorafin da Daraktan Al’amuran Fadar gwamnatin jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo ya shigar, inda ya zargi ɗan jaridar da ɓatanci da ɓata masa suna ta cikin rahotannin da ake yaɗawa a Dan’uwa Rano TV, wata kafar yaɗa shirye-shirye ta yanar gizo.

Rahotanni sun ce, an gayyaci Ɗan’uwa Rano zuwa shalkwatar ƴan sanda ta Zone One a Kano a ranar Asabar, inda aka yi masa tambayoyi kan waɗannan zarge-zargen.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da bincike kan Mista Rogo, wanda ake zargin yana ƙarƙashin binciken Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) bisa zargin ɓarnar kuɗaɗe da suka shafi kwangiloli da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 6.5.

A halin yanzu, ƙungiyoyin ƴan jarida da na farar hula a Kano sun yi tir da tambayar da aka yi wa Ɗan’uwa Rano, inda suka bayyana hakan a matsayin yunƙuri na tsoratar da kafafen yaɗa labarai da toshe muryoyin masu sukar gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa an kama shi ne a ranar Asabar bisa umarnin Abdullahi Ibrahim Rogo, Darakta Janar a Fadar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kamar yadda Hikima RTV ta ruwaito.

By Babaji