Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Iyalan wasu jami’an soji da ake tsare da su bisa zargin shirya juyin mulki sun gudanar da zanga-zangar lumana a harabar Majalisar ƙasa a ranar Laraba, inda suka buƙaci a gaggauta gurfanar da su a kotu ko kuma a sake su.
Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa matan aure da yara da dama sun taru a ƙofar shiga Majalisar, suna tafiya a hankali tare da riƙe allunan da ke ɗauke da saƙonni kamar “Kada ku kashe mana iyayenmu,” “Tsare mutum ba tare da shari’a ba zalunci ne,” da kuma “Watanni shida na azaba: ya isa haka.”
Cikin kuka da rawar murya, yaran sun roƙi a yi musu adalci tare da ba su damar ganin iyayensu, inda suka ce sun shafe watanni ba su gan su ba.
‘Yar shekara takwas, Halima Muhammad, ‘yar Lt Col Muhammad Almakura, ta ce: “Don Allah kada ku kashe mana baba. Muna son a yi masa adalci.
“Tun lokacin da gwamnati ta kama shi, rayuwarmu ta canza. Mahaifiyata tana kuka kullum. Ina kewarsa sosai.”
Shi ma Ibrahim Bala mai shekara tara, ɗan Major Bala, ya nuna kewarsa: “Don Allah gwamnati ta dawo mana da baba lafiya.
“Na ƙarshe da na gan shi watanni tara da suka wuce. Ina kewarsa sosai. Yana koya min abubuwa na makaranta da yadda yara ke mu’amala da manya.”
Ya ƙara da cewa: “Ina aji huɗu a firamare, amma na ƙarshe da na gan shi watanni shida da suka wuce. Gidanmu ya zama shiru ba tare da shi ba. Ina kewarsa domin shi ne ke fita da ni yawon shaƙatawa.”
Fatima Yusuf mai shekara huɗu, ‘yar Wing Commander Yusuf, ta yi roƙo ga shugabannin ƙasa: “Ina roƙon Shugaban ƙasa da Uwargidan Shugaban ƙasa su dawo mana da babana lafiya. Tun da ya tafi, babu wanda nake wasa da shi. Yana koya min abubuwa kuma yana fita da ni.”
Nana Aisha Usman mai shekara 11 ta buƙaci gwamnati ta saki su ko ta gurfanar da su a kotu: “Don Allah ku taimaka ku roƙi gwamnati ta saki babana ko ta kai shi kotu. Shi da sauran da aka tsare sun cancanci adalci.
“Tun da aka tafi da shi, gidanmu ya zama babu kowa. Yana fita da ni kasuwa yana saya min abubuwa, kuma yana taimaka min da aikin gida. Ban yarda babana mutum mara kirki ba ne. Ina so gwamnati ta bincika ta sake shi.”
Daya daga cikin matan aure, Nana Ibrahim, ta ce yadda aka kama su da ci gaba da tsare su yana da tambaya: “Dukkan zargin juyin mulki da kama su abin tambaya ne. An shafe sama da watanni shida ana bincike.
“Amma har yanzu ba a ba su damar ganin iyalansu ko lauyoyinsu ba. Idan akwai hujja, su fito da ita a fili.
“Su bayyana wa duniya nawa ne ke tsare, su kai su kotu. Abin da muke nema kenan.
“Sun ce sun gama bincike, to me ya sa ake jinkiri? Su kai su kotu su gabatar da hujjoji.
“Muna son shari’a a bude, kowa ya ji tuhumar, kowa ya kare kansa. Idan aka tabbatar ba su da laifi, a sake su. Ya isa haka!”
Wannan zanga-zanga na zuwa kusan wata guda bayan da iyalan suka roƙi Shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ba su damar ganin mazajensu, ko a sake su ko a kai su kotu.
An yi wannan roƙo ne a wani taron manema labarai a Abuja da matan aure sama da 20 da yara da dama suka halarta, ciki har da jariri mai watanni biyu.
Iyalan sun samu rakiyar lauyan kare haƙƙin ɗan Adam Deji Adeyanju da kuma ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore.
A wajen taron, sun ce an tsare jami’an na sama da kwanaki 160 ba tare da shari’a ko hulɗa da iyalansu ba, abin da suka kira take haƙƙinsu na asali.
A madadin iyalan, Memuna Bashiru ta ce tsawaita tsare su ya jefa gidajensu cikin damuwa da rashin tabbas, inda ta ce duk da ana yada zarge-zargen a fili, iyalan ba su san halin da mazajensu ke ciki ba.
Sun roƙi Shugaban ƙasa da Uwargidansa Oluremi Tinubu da su sa baki, suna cewa abin da suke nema ba alfarma ba ne, illa bin doka.
An fara sanar da kama jami’an ne a ranar 4 ga Oktoba, 2025, daga bakin tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Soji, Brig Gen Tukur Gusau, wanda ya ce an kama jami’ai 16 bisa zargin karya dokokin soja da rashin ɗa’a.
Sai dai wani bincike daga baya ya nuna akwai wata ƙungiya ta sirri ta jami’an soji da ake zargin suna shirin juyin mulki, ƙarƙashin jagorancin wani babban jami’i.
Rahotanni sun ce shirin ya haɗa da bibiyar muhimman wurare kamar Fadar Shugaban ƙasa, hedkwatar rundunar soji, barikin Niger a Abuja da filayen jiragen sama, tare da tsara ranar 25 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranar aiwatarwa.
Daga cikin waɗanda ake tsare da su akwai Brig Gen M. A. Sadiƙ, Col M. A. Maaji, Lt Col S. Bappah, Lt Col A. A. Hayatu, Lt Col P. Dangnap, Lt Col M. Almakura, Maj A. J. Ibrahim, Maj M. M. Jiddah, da Maj M. A. Usman.
Sauran sun haɗa da Maj D. Yusuf, Capt I. Bello, Capt A. A. Yusuf, Lt S. S. Feliɗ, Lt Cdr D. B. Abdullahi, Sƙn Ldr S. B. Adamu da Maj I. Dauda.
Rahotanni sun ce shirin juyin mulkin ya nufi manyan jami’an gwamnati ciki har da Shugaban ƙasa Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima.
