Zargin kisan Kiristoci da barazanar Trump

Spread the love

A cikin ’yan kwanakin nan, shugaban Amurka Donald Trump ya tsunduma cikin furuci mai tada hankali, yana zargin cewa ana kashe Kiristoci a Nijeriya, tare da yin barazanar kai farmaki ga ƙasar idan gwamnati ba ta kawo ƙarshen abin da ya kira “kisan aƙidar addini” ba. Wannan magana ba wai kawai ta yi nisa da gaskiya ba, har ma tana iya tada rikici da rarrabuwa kai a ƙasa da tuni take fama da ƙalubalen tsaro.

Wannan batu ne mai hatsarin gaske, saboda ƙarya ce mai son ta zama gaskiya da ƙarfin tsiya. Aka ce ana kashe Kiristoci a Nijeriya — su Kiristocin Nijeriya suka fito suka ce “ba haka ba ne”. Aka ce za a cafke ƙasar da makami — gwamnati ta ce “Nijeriya ƙasa ce mai doka da girma, ba filin gwaji ba.” Wannan saɓani ne tsakanin hayaniya da hujja, tsakanin tashin hankali da hikima.

Abin farin ciki shi ne Gwamnatin Nijeriya ta nuna nagartaccen shugabanci: ta tsaya kan hujjoji, ba kan hayaniya ba. Fadar Shugaban ƙasa ta tunatar da duniya cewa Nijeriya ƙasa ce mai doka da tsarin addini mai ’yanci, kuma cewa ƙalubalen tsaro da ake fuskanta ba na addini kaɗai ba ne — matsala ce da ta shafi Musulmi da Kiristoci gaba ɗaya. Wannan shi ne gaskiya, kuma shi ne abin da shugabanni na ɓangarorin addinai a cikin ƙasar ma suka tabbatar.

Idan akai la’akari da tarihin siyasar duniya, ba sabon abu ba ne ga wasu manyan ƙasashe su yi ƙoƙarin sanya matsin lamba da labaran ban tsoro wajen cimma manufofinsu. Amma Nijeriya ba ƙasar da za a razana da furucin siyasa ba ce. Tsayuwar da gwamnatin ta yi — cikin izza, cikin mutunci, da cikin hikimar diflomasiyya — shi ne abin da ya dace. Jin tsoron kai farmaki ba matsala ba ce; amsa da natsuwa ita ce alamar ƙarfi.

A nan ba ana musanta cewa babu matsalar tsaro a wasu yankuna ba ne. Amma fa ba adalci ba ne a kauda kai daga rayukan dubban Musulmi da aka kashe a hare–haren ’yan ta’adda da masu tayar da hankali. Ta yaya za a ce ana kare adalci idan aka ce rayukan ɓangare guda su ne kawai abin tausayawa? Gaskiya bata da fuska — kuma wanda ke neman kare addini da gaskiya ba zai yi watsi da gaskiyar ɗayan ɓangare ba.

Amurka da kanta tana fama da rikicin tsaro, rikicin addini, da maƙiya ciki da wajen gida. Shin idan wata ƙasa ta ce tana shirin kai farmaki a can saboda rikicin #BlackLiɓesMatter, da ba za a kira ta hauka ba? Don me to a zo a yi mana magana da rashin girmamawa irin haka?

Matsayar Trump, wacce ta cika da kalaman tayar da hankali, ta nuna yadda siyasar cikin gida ta Amurka kan iya yin tunani marar kan gado. Amma ga Nijeriya, wannan lokaci ne na nuna cewa ƙasa mai mutunci tana iya kare kanta ba tare da tsoro ko zafin rai ba. Tsaro yana buƙatar haɗin kai, tsari, da gudunmawar kowa, ba barazana daga nesa ba.

’Yan Nijeriya su san wannan: ƙasarmu tana cikin tafiyar farfaɗo da tsaro, kuma ta hanyar aiki tare, haɗin kai, da jajircewa za a cimma nasara. Barazana daga waje ba za ta kawar da ƙalubalen ba — illa ta ƙara munin al’amura. Don haka, mu tsaya tare da ƙasarmu, mu goyi bayan tsarin tsaro, mu kuma guji barin wani ya yi mana barazana da iƙirarin ƙarya.

A wannan lokaci, Nijeriya ta yi abin da ya dace: ta kare martabata, ta kare gaskiya, ta kuma nuna cewa ita ƙasa ce mai cikakken ikon kanta. Wannan ne muryar ƙarfi — kuma wannan ne abin da ya kamata kowane ɗan ƙasa nagari ya tsaya a kai.

By ukarofi