*Ya yi maraba da rage ma ta hukunci
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shahararren malamin addinin Musulunci, Shaikh Ahmad Gumi, ya yi maraba da sauya wa Maryam Sanda hukunci daga kisa zuwa zaman shekaru 12 a gidan yari, yana mai cewa nadamar da ta nuna bayan kisan mijinta alama ce ta “aikin Shaiɗan”.
Shaikh Gumi ya bayyana haka a wani saƙon da ya wallafa a Facebook, inda ya ce kisan mijin nata, Bilyaminu Bello, ya faru ne da tsananin fushi da tasirin Shaiɗan, sannan kuma ta fashe da kuka bayan ta gane abin da ta aikata — abin da ya kira babban alamar nadama.
A ranar Laraba ne Fadar Shugaban ƙasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya janye cikakken afuwar da aka yi wa Maryam Sanda a baya, amma ya sauya hukuncinta zuwa ɗauri na shekaru 12 saboda tausayi da kuma la’akari da yaran da ta bari.
Shaikh Gumi ya kare matakin, yana mai cewa dangin mamacin sun riga sun yafe mata, kuma hakan ya dace da ƙa’idojin shari’ar Musulunci.
A cewarsa, a Musulunci yafiya alama ce ta rahama kuma tana da daraja mafi girma a gaban Allah fiye da ramako ko ɗaukar fansa.
Ya ce, adalci a Musulunci ba a shimfiɗa shi kan fushi ko ɗabi’ar ɗaukar fansa ba, sai dai daidaito, hikima da tausayi. Ya yi addu’ar Allah ya kare al’umma daga irin waɗannan fitintinu.
Idan za a iya tunawa, Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan Maryam Sanda, kamar yadda Babbar Kotu da Kotun ɗaukaka ƙara suka yanke mata, amma yafe mata da Gwamnatin Tinubu ta yi tare da wasu masu laifukan daban-daban ya janyo cece-kuce da allawadai a faɗin ƙasar.
