Daga IBRAHIM HAMISU a Kano.
Ƙungiyar Hausa ta sashen koyar da harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero da ke Kano, ta ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen gudanar da bikin makon Hausa na shekarar 2026, wanda aka tsara domin bunƙasa harshen Hausa, al’adunsa da kuma ƙarfafa amfani da shi a fannoni daban-daban na rayuwa.
A wani ɓangare na shirye-shiryen, shugabannin ƙungiyar sun kai ziyarar ban-girma ga fitaccen marubuci kuma shugaban Mawallafa na Arewa da masu shirya fina-finai ta jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON inda suka tattauna kan muhimmancin bikin da kuma gudummawar da masu ruwa da tsaki za su bayar wajen ganin an cimma manufofinsa.
Za dai a yi taron ne a ranar Talata 17 da watan Nuwamba 2026 , da ƙarfe 10 na safe Jami’ar Bayero Kano (newsite) wanda aka gayyato manyan masana da mawaka da ƴan Fim.
Ziyarar ta gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Abba Dauda Ahmad, tare da mataimakinsa na farko, Ibrahim Hamisu, wanda ma’aikaci ne a jaridar Blueprint Manhaja na Kano da mataimakiyarsa ta biyu, Aisha Musa, da membobi da dama, waɗanda suka bayyana muhimmancin haɗin gwiwar masana, marubuta da masu shirya fina-finai wajen bunƙasa harshen Hausa da al’adunsa.
Sun bayyana cewa, bikin Makon Hausa wani muhimmin shiri ne da ake gudanarwa duk shekara domin wayar da kan al’umma kan darajar harshen Hausa, tare da samar da dama ga ɗalibai da masana su tattauna hanyoyin bunƙasa harshen da kuma kare al’adun Hausawa daga abubuwan da ka iya kawo musu koma-baya.
Haka kuma, ƙungiyar ta kai ziyara ga uban ƙungiyar, Dakta Nura Salihannur, wanda ya nuna jin daɗinsa tare da yaba wa shugabannin bisa jajircewarsu da ƙoƙarin da suke yi wajen inganta harshen Hausa. Ya kuma yi musu nasiha da su kasance masu riƙo da amana, haɗin kai da jajircewa wajen gudanar da ayyukan da za su amfani harshen da al’ummar Hausawa baki ɗaya.
A yayin ziyarar, Dakta Nura ya ƙarfafa musu gwiwa da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukan raya Hausa da al’adunta, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da shirya shirye-shiryen da za su ƙara wa harshen martaba, musamman a tsakanin matasa da ɗaliban jami’o’i.
A wani mataki na ci gaba da neman haɗin gwiwa, ƙungiyar ta kuma kai ziyara ga shugaban cibiyar bincike kan harsunan Nijeriya, fassara da adabin gargajiya, Farfesa Maryam Mansur Yola, domin ƙarfafa dangantaka da neman goyon bayan cibiyar wajen ganin bikin Makon Hausar ya gudana cikin nasara.
