Ƙaramar Hukumar Ɓagwai ta yi fice wajen noma da kiwo – Hon. Belllo Gadanya 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban ƙaramar Hukumar Ɓagwai, Hon. Bello Abdullahi Gadanya ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam bisa shirya taron kalankuwa na nuna al’adu na gargajiya da sana’oi da ake tun kaka da kakanni.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a rumfar ƙaramar hukumar Bagwai da suka bajekolin kayayyaki da suke nomawa.

Ya ce sun kawo abinda suke nomawa a  yankin da ke da tasiri a noma da abinda suke da su na gargajiya sun bajekolinsu jama’a sun gani.

Shugaban na ƙaramar hukumar na Ɓagwai ya yi nuni da cewa yankin ya yi fice wajen noma na  rani da damina, suna da katafaren dam da suke noma kayan lambu da kiwon kifi ko a ‘yan  kwanaki baya ma ƙaramar hukumar ta sahale an su yi tarin kifaye masu yawa na kiwo masu saurin hayayyafa an zuba a cikin dam ɗin.

Hon. Bello Abdullahi Gadanya ya ce taron nuna al’adu, mataki ne na inganta kimar al’ummarmu da nuna irin sana’oi da muka gada  muke alfahari da wanzuwarsu har yanzu kuma zai amfanar da matasa masu tasowa.

By ukarofi