Riƙo da al’adun gargajiya zai ƙara mana mutunci a idon duniya – Hon. Tukur Wada 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana farfaɗo da al’adun mu na gargajiya da ware ranaku na musamman a jihar Kano aka yi biki a kai wani muhimmin abu ne mai kyau da Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta yi na kyakkyawan tunani abin alfahari da farin ciki da isar da muhimmin saƙo na al’adunmu ga duniya.

Shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon.Tukur Muhammad Wada ne ya bayyana hakan a yayin taron da aka yi a harakar filin kasuwar bajekoli ta Kano ya ƙara da cewa kamar a masarautar su ta Rano suna da kyakkyawan tarihi na sarauta da zamantakewa da sana’o’i da suka yi fice akai  don haka suna matuƙar murna da wannan taro na farfaɗo da al’adu.

Ya ce su a matakin ƙaramar hukumar Rano za su cigaba da raya  al’adun gargajiya ta fito da abubuwa da ba a sani ba na al’adun al’ummar su, domin matasa da yara na na baya masu tasowa su sani su riƙe su yi alfahari da su.

Hon. Tukur Muhammad Wada ya yi kira ga al’ummar Rano da ma jihar Kano gabaɗaya akan su san muhimmancin cewa riƙo da kyawawan al’adu da suka gada yana da muhimmanci kuma zai daɗa ƙara musu kima da mutunci a idon duniya muddin suka riƙe shi da kyau.

By ukarofi